Garabasa: Matashi na neman budurwar da zata so shi, zai ba ta albashin N150k duk wata
- Wani matashi ya bayyana kudurinsa na neman masoyiya da zata so shi shi kuwa yake bata albashi
- Ya kuma ce, bayan albashin mai tsoka, zai hada ba sauran tagomashin alawus-alawus na kasancewa masoyiya
- Ya bayyana haka ne a kafar sada zumunta, lamarin da ya jawo cece-kuce da martanin jama'a
Wani matashi dan Najeriya wanda aka bayyana da suna Chudy mai amfani da suna @OkparaNnaJiAku a kafar sada zumunta ya ce yana neman budurwa wacce za ta fahimceshi ta yadda zai ke ba ta N150,000 a matsayin albashin wata-wata.
Chudy ya kuma nuna cewa adadin kudin zai rinka karuwa bayan watanni uku kuma zai ba da wasu karin garabasa da fa'idojin da suka hada da karin wata na 13, fansho, da sauransu.
Saurayin, wanda bayanansa suka nuna shi dan gwagwarmayar yanar gizo ne wanda ya ci lambar yabo, manazarcin bayanai, fasaha, masanin kudaden crypto da sauransu, ya ce duk mace mai sha'awar yin abin da ya bukata, kawai ta nuna alama.
Maganarsa ta haifar da dimbin martani daga mutane sama da dubu biyu a lokacin da ya wallafa rubutun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli martanin mutane kan wannan batu
Legit.ng ta tattaro yadda mutane suka yi martani kan bukatar tasa mai jan hankali.
@hackSultan ya ce:
"Ka ninka albashin da fa'idojin ninki biyu tare da samun sabon MacBook din ranka yake so, iPhone da AirPods yayin da suka iso. Amma matsayi shine 'yan matan gefe."
@Sntcele ta ce:
"Maimakon duk wannan albashi da alawus, me zai hana ka koya mani yadda ake samun kudi saboda in ka guje ni in yi kuka kadan."
@chisom_loveth ya ce:
"Da fatan ba za ka damu da fuskar mai dinkin kaya ba. Gara ma, idan ka samu, na tabbata za ta so wasu daga cikin tufafinmu na siyarwa."
Murna ya lullube mahaifiyar tagwaye 'yan kwalisa da suka zama likitoci a rana daya
A wani labarin kuwa, wasu samari kyawawa guda biyu, Chidimma Muogbo da Chinemerem Muogbo, wadanda tagwaye 'yan uwan juna ne sun kammala karatu a makarantar likitanci a matsayin likitoci.
Mahaifiyarsu, Uju Sussan mai digirin digirgir kuma babbar malama a Jami'ar Jihar Anambra ta Najeriya, ita ta yada labarin a shafinta na LinkedIn.
Baya ga taya 'ya'yanta maza biyu murna, mahaifiyar cikin alfahari ta kuma bayyana yadda suka fuskanci kalubale tare da dandamali daban-daban na kafofin sada zumunta da kuma tsarin tantancewa saboda kamanceceniyarsu.
Asali: Legit.ng