Matsalar Tsaro: Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Mayakan Boko Haram a Yobe

Matsalar Tsaro: Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Mayakan Boko Haram a Yobe

  • Sojojin Najeriya sun fafata da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne a Babbangida dake jihar Yobe
  • Mazauna garin Babbangida, Hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa, sun tsorata da harin, inda suka tsere cikin jeji
  • Rahotanni sun nuna cewa wani soja ɗaya ya samu raunuka a fatatawar, kuma ana cigaba da bashi kulawa

Yobe - Dakarun soji na rundunar sojojin Najeriya sun fatattaki gungun mayakan Boko Haram ranar Laraba a jihar Yobe..

Wata majiya mai karfi daga cikin rundunar ta shaidawa Channels tv cewa sojojin sun samu nasarar kwato motar Toyota ɗaya daga cikin uku da mayakan suka zo da su.

Sai dai soja ɗaya ya samu rauni inda yake cigaba da amsar kulawar lafiya bayan harin yan ta'addan.

Dakarun sojojin Najeriya
Matsalar Tsaro: Dakarun Sojoji Sun Yi Artabu da Mayakan Boko Haram a Yobe Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An yi wannan artabu ne yayin da yan Boko Haram suka yi kokarin kutsawa garin Babbangida, hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

An Yi Kazamin Arangama Tsakanin Yan Tasha Da Yan Kasuwa, Ana Fargabar Rasa Rayyuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna garin sun tsorata

Wani mazaunin garin Babbangida, Audu Yakubu, yace maharan sun zo a motocin ɗaukar kaya Toyota guda uku, inda suka tunkari sansanin sojoji kai tsaye.

Yakubu yace:

"Wasu yan kauye sun ankarar da mu cewa sun ga bakin fuska a kan hanyar Babbangida, saboda haka muna ganin isowarsu muka tsere cikin jeji don tsira da rayuwarmu."

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa yace maharan sun farmaki garin ne da misalin karfe 6:15 na yamma, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Sai dai a bayaninsa yace dakarun soji sun kawo ɗauki cikin gaggawa inda suka maida martani, a ka yi musayar wuta tsakaninsu.

Babbangida yana da nisan kilomita 50 daga garin Dapchi, inda a baya wasu mahara suka sace ɗalibai mata 110 daga makarantar sakandiren mata a watan Farairun shekarar 2018.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Jami'ar jihar Kwara, Su Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

Punch ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:00 na dare, lokacin wasu mutane a cikin mota suka yi awon gaba da ɗalibar yar 200-Level.

Legit.ng Hausa ta gano cewa ɗalibar mai suna Khadijat Ishaq, ta na kan hanya tare da kawarta zuwa dakin kwanan su dake wajen makaranta yayin da aka farmaketa aka sace ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel