Ba ma son a kama sunan wani kan kisan musulmai a Jos, Kwamishinan 'yan sandan Filato

Ba ma son a kama sunan wani kan kisan musulmai a Jos, Kwamishinan 'yan sandan Filato

  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Filato ya magantu kan wadanda suka hallaka musulmai a Jos
  • Ya ce ba wannan ne karon farko ba, amma hukumar 'yan sanda ba ta son a kama sunan kowa cikin lamarin
  • Ya kuma ba da tabbacin cewa, hukumar na aiki tukuru wajen ganin an zakulo wadanda suka aikata laifin

Jos, Filato - Kwamishinan ‘yan sandan Filato, Edward Egbuka, ya ce duk da cewa harin da aka kai kan matafiya a Jos ranar Asabar ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ya faru ba, 'yan sanda ba sa son a kama sunan kowa a lamarin.

Ya lura cewa wadanda suka kai farmaki kan matafiyan a Jos a ranar 14 ga watan Agusta 'yan ta'adda ne da 'yan daba wadanda ke son dagula yanayin tsaro a jihar don haifar da matsala da sace-sace.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Shugaban hukumomin tsaro a jihar ga Gwamna Simon Lalong.

Ba ma son a kama sunan wani kan kisan musulmai a Jos, Kwamishinan 'yan sandan Filato
Taswirar jihar Filato | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Gwamna Dr Makut Macham ya fitar a Jos, Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

“Wadannan 'yan ta'adda ne da 'yan daba wadanda suke son dagula yanayin tsaro don haifar da matsala da sace-sace.
“Wannan ba shine karo na farko da haka ta faru ba. Ba ma son mu ambaci sunan kowa.”

A cewarsa, an ceto mutane 36 ba tare da sun ji rauni ba daga harin kuma suna cikin koshin lafiya, ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike tare da kama mutanen da suka aikata laifin.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Ya ba da tabbacin cewa hukumomin tsaro za su zakulo masu laifi da bata gari kuma a sanya su fuskantar fushin doka.

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Filato, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya musulmai 25 a hanyar Rukuba, a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.

Rev. Fr. Polycarp Lubo, shugaban CAN a jihar, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka aikata danyen aikin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Legit Hausa ta rahoto cewa wasu matasa da ake zargin 'yan Irigwe ne sun kai hari kan motocin bas guda biyar dauke da matafiya Musulmai sama da 90, sun kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

Kara karanta wannan

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel