Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

  • Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi ya magantu a kan lamarin tubabbun 'yan Boko Haram
  • El-Kanemi ya ce zai yi wahala matuka su yarda da sake karbar 'yan ta'addan da suka tuba a cikin garuruwansu
  • Ya bayyana cewa mutane za su kasance cikin fargaba na tashin hankalin da suka shafe shekaru 12 suna fama da shi

Shugabannin gargajiya da na addini a Borno sun ce zai yi wahala a sake karbar 'yan Boko Haram da suka tuba cikin garuruwa su.

Shugabannin sun bayyana fargaba kan yadda sojojin Najeriya za su raba tubabbun 'yan Boko Haram da tsattsauran ra'ayi a karkashin shirin su na Safe Corridor, jaridar The Cable ta ruwaito.

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno
Shehun Borno ya ce ba za su taba mantawa da barnar da Boko Haram tayi masu ba Hoto: Nigeria Army HQ
Asali: Facebook

Abubakar El-Kanemi, Shehun Borno, ya ce wannan abu ne mai kyau, amma mutane za su ci gaba da kasancewa cikin fargaba na bala'in tashin hankalin da aka shafe shekaru 12 ana yi, musamman mazauna garuruwan da za a mayar da masu tayar da kayar bayan.

Kara karanta wannan

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

Ya ce:

“Shirin Safe Corridor na Sojoji ya kai ga kawar da tsattsauran ra’ayin tubabbun ‘yan ta’adda a jihar Gombe. Amma zai yi matukar wahala mu sake karbar tubabbun ‘yan ta’addan cikin garuruwanmu da aka lalata.”

Ya kara da cewa Boko Haram sun lalata garin Bama da kwalejin ilimi a watan Satumba, 2014.

An rahoto cewa maharan sun kashe hakimai 13 da masu unguwanni da dama a kananan hukumomi 16 na Borno.

Shehun Borno ya kara da cewa:

"Abu ne mai sauki a gafartawa asarar rayuka da dukiyoyi da yawa, amma yana da wahala a manta da asarar rayuka a cikin garuruwa daban -daban na Masarauta ta.
“An kashe mutane da yawa tare da kadarorinsu na tsawon shekaru 12. Kuma ku mutane da kafafen watsa labarai kuna sanya ran mu manta sannan kuma mu yafe wa 'yan ta'adda da suka tuba? "

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

A gefe guda, tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Soji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma'a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura 'yan ta'addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.

A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'Ku dauki 'yan ta'addan Boko Haram da suka tuba a matsayin fursunonin yaki', jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel