Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki

Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki

  • Gwamna Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi Allah wadai da matakin da majalisar dattawa ta dauka na mika ikon INEC ga NCC
  • Da yake magana game da batun aika sakamakon zaben ta hanyar na’ura, gwamnan na jihar Sakkwato ya ce ba za a iya raba ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa INEC tare da NCC ba
  • Sai dai kuma, Tambuwal, ya jinjinawa majalisar wakilai kan yanke shawarar gayyatar INEC don ta yi magana game da shirinta na amfani da tsarin tura sakamakon zabe ta na’ura

Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sakkwato, ya ce matakin da Majalisar Dattawa ta dauka na mika ikon INEC na gudanar da zabe ga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ya saba wa tsarin mulki.

Tambuwal, wanda ya kasance tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin Sallah: Wani gwamna ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade

KU KARANTA KUMA: Shugaban EFCC ya yi kakkausar gargadi ga jami’an hukumar

Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki
Gwamna Tambuwal ya ce shawarar da majalisar dattijai ta yanke na mika ikon da kundin tsarin mulki ya ba INEC na gudanar da zabe ga NCC ya saba wa tsarin mulki. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Tambuwal ya ci gaba da cewa ba za a iya raba ikon da kundin tsarin mulki ya ba INEC da kowace hukuma ba.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Don kaucewa shakku, S.78 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa 'Rijistar masu jefa kuri'a da gudanar da zabe za su kasance karkashin shugabanci da kulawar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa."
“A cikin Jadawali na Uku, Sashi na 1, F, S.15: INEC na da ikon shiryawa, aiwatarwa da kuma lura da dukkan zabuka.
"Kundin Tsarin Mulki ya ci gaba da cewa ayyukan INEC ba za su kasance karkashin jagorancin wani ko hukuma ba."

Gabatar da sakamako ya kasance bangare mai matukar muhimmanci a zabe

Gwamna Tambuwal ya kuma bayyana yanayin yadda zaben ke gudana da kuma yadda ake tura sakamakon zaben ya kasance wani muhimmin bangare na gudanarwa, sa ido, aiwatarwa da kuma shirya zabuka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta gaza magance matsalar tsaro - Kukah ya fada wa Amurka

Ya bayyana cewa duk da cewa majalisar kasa na da ikon fitar da tsarin doka, amma ya zama dole ya dace da Kundin Tsarin Mulki, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Tambuwal ya yaba wa majalisar wakilai saboda gayyatar INEC

Duk da haka, Gwamna Tambuwal ya yaba wa shugabanni da mambobin majalisar kan shawarar da suka yanke na gayyatar INEC don yin jawabi ga majalisar da ma kasa kan shirye-shiryenta a shekarar 2023 na amfani da tsarin tura sakamakon zabe ta na’ura.

KU KARANTA KUMA: Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP

Ya yaba wa majalisar kan shawarar da ta yanke, yana mai cewa tana tattare da hikima.

Gwamnan ya kara gargadin su da su ci gaba da kasancewa a kan turbar kishin kasa da zurfafa dimokiradiyyar Najeriya ta hanyar karfafa tsarin zabe na gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Ya ce babban abin da ya fi dacewa game da tura sakamakon zabe ta na’ura shi ne barin lamarin a hannun INEC.

Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura

A gefe guda, mambobin Jam’iyyar APC a majalisar dattijai a ranar Alhamis sun kada kuri’ar kin amincewa da aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura, Punch ta ruwaito.

Kwamitin Majalisar a cikin rahotonsa ya ba da shawarar a Sashe na 52 (3) cewa, INEC “na iya tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura in akwai damar yin hakan.”

Amma wani sanatan APC daga Jihar Neja ta Arewa, Sabi Abdullahi, ya gyara ayar dokar zuwa, “INEC na iya yin la’akari da tattara sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa, in har aka yi la’akari da cewa tsarin sadarwar na kasa ya kai gwadaben da Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta aminta da shi kuma Majalisar Tarayya ta amince da hakan.”

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng