Shirin Sallah: Wani gwamna ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade
- Gwamnan jihar Borno ya rabawa talakawa da gajiyayyi kudade gabanin babbar sallah mai zuwa
- Gwamnan ya kuma biya albashin ama'aikata domin kowa ya samu hanyar yin sallah cikin walwala
- Wannan batu na zuwa ne yayin da ake shirin babbar sallah da take tafe a mako mai zuwa idan Allah ya kaimu
A ci gaba da shirye-shiryen babbar sallah mai zuwa, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya amince da biyan dukkan albashin watan Yuli nan take ga dukkan ma'aikatan gwamnati a fadin jihar.
Hakazalika gwamna Zulum ya fitar da sama da N100m don rabawa bangarori daban-daban na Mutanen da ke fama da nakasa (PLWDs).
Sama da Naira N100m ga masu karamin karfi a matsayin wani bangare na abinda Gwamnati mai ci yanzu ta kirkiro, wanda galibi Kwamishinan Wasanni da Ci gaban Matasa, Hon Saina Buba ke rabawa.
KARANTA WANNAN: Hukumar Sojoji ta saki yan ta'addan Boko Haram 1009, ta mikasu ga gwamnatin Borno
Jaridar Vanguard ta lura cewa Zulum ya gyara tsarin biyan albashi bayan karbar mulki a hannun Sanata Kashim Shettima inda yake biyan kafin 25 ga kowane wata.
Tallafin na sama da Naira miliyan 100 da aka kirkiro an ce an ba da shi ne ga masu rauni a cewar Kwamishina Buba, don rage radadin fatara da wahalhalu domin gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin walwala.
Wadanda suka ci gajiyar shirin
A wannan karon, wadanda suka ci gajiyar shirin sun hada da Kurame da Kutare 418, yayin da nakasassu 454 suka samu N15,000 zuwa N20,000 kowannensu, ya danganta da halin da ake ciki.
Da sanyin safiyar yau Alhamis 15 ga watan Yuli, Hon Saina Buba wanda ya jagoranci mambobin tawagarsa zuwa Cibiyar Bita ta Makanta a cikin Maiduguri ya kirga makafi 1,095 wadanda ke da matsalar bude asusun ajiya, saboda haka aka basu kudinsu a hannu.
A wurin rabon, bincike ya nuna cewa, an zagulo nakasassun bogi sama da 300 cikin dandazon na mutane.
Wannan ya tilasta Kwamishina neman kudi kuma ya magance matsalar nan take.
Amma don kauce wa irin wannan yanayi a nan gaba, Hom Saina Buba, shugaban kungiyar, ya ce:
"Za a dauki tsauraran matakan biyan kudi don kaucewa samun masu karba sau biyu ko hargitsi a cikin tsarin."
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin yayin bayyana wa wakilin Vanguard yadda suka ji, sun nuna godiyarsu ga gwamna Zulum kan yadda yake nuna himma ga ma'aikatan gwamnati da kuma masu karamin karfi a cikin al'umma.
KARANTA WANNAN: Badakala: Hukumomin gwamnatin tarayya sun karkatar da N300bn, Majalisa ta dauki mataki akai
Babbar Sallah: Dillalan raguna sun fara kokawa, sun ce ga raguna birjik babu mai saye
A wani labarin, 'Yan kwanaki kadan kafin gudanar da bikin Babbar Sallah, dillalan ragunan layya sun fara koka rashin ciniki yadda ya kamata a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Daily Trust ta ruwaito.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), wanda ya ziyarci wasu kasuwannin raguna a sassa daban-daban na llorin a ranar Alhamis ya ruwaito cewa dillalan ragunan da dama sun koka da karancin ciniki.
Akwai adadi masu yawa na raguna a dukkan kasuwannin da aka ziyarta, inda dillalan ke jiran masu siye da jiran tsammani.
Asali: Legit.ng