Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura

Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura

  • Ilahirin sanatocin APC ne suka yi watsi da aika sakamakon zaben ta hanyar na’ura
  • Sanatoci 88 ne suka kasance a zauren sannan sune suka kada kuri’ar
  • Hukumar sadarwar Najeriya, NCC ta ce kashi 43 ne kadai na fadin kasar nan ke da maganadisun sadarwa

Mambobin Jam’iyyar APC a majalisar dattijai a ranar Alhamis sun kada kuri’ar kin amincewa da aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura, Punch ta ruwaito.

Kwamitin Majalisar a cikin rahotonsa ya ba da shawarar a Sashe na 52 (3) cewa, INEC “na iya tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura in akwai damar yin hakan.”

Amma wani sanatan APC daga Jihar Neja ta Arewa, Sabi Abdullahi, ya gyara ayar dokar zuwa, “INEC na iya yin la’akari da tattara sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa, in har aka yi la’akari da cewa tsarin sadarwar na kasa ya kai gwadaben da Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta aminta da shi kuma Majalisar Tarayya ta amince da hakan.”

Mambobin Kwamitin Sadarwa sun sanar da zauren majalisar a baya cewa NCC ta bayyana cewa kashi 43 cikin 100 na kasar ne kawai ke da isasshen maganadisun sadarwa sosai.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, ya yanke hukuncin amincewa da gyaran yayin da ya gudanar da kuri’ar jin ra’ayin ‘yan Majalisar.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Sanatoci sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura
Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura Hoto: @NGRSenate
Asali: UGC

KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD

An samu sabani kuma Shugaban marasa rinjaye, Enyinnaya Abaribe, ya yi kira da a raba zauren wanda zai bukaci kowane dan majalisar ya jefa kuri'arsa.

Shugaban Majalisar ya yi na’am da bukatar Abaribe inda ya yi kira da a raba zauren.

A karshen kuri’ar, sanatoci 88 sun jefa kuri'a, yayin da 28 ba su kasance a zauren Majalisar ba, rahoton ya kara.

PDP ta ce a, APC ta ce a'a

Sakamakon zaben ya nuna cewa sanatocin Jam’iyyar APC 52, ciki har da shugaban kwamitin majalisar dattijai na INEC, Kabiru Gaya, sun nuna rashin amincewa da rahoton kwamitin, wanda ya bai wa hukumar zaben ikon ita a kashin kanta ta yanke hukunci kan yiwuwar aiwatar da aika sakamakon zaben ta hanyar na’ura.

Mambobin jam’iyyar PDPn da ke kasa duk sun kada kuri’ar amincewa da aika sakamakon ta yanar gizo ga hukumar zaben ba tare da sa baki daga hukumar NCC ko majalisar kasa ba.

Sanatocin PDP sun ce barin hukumar NCC da majalisar kasa su yi katsalandan cikin harkokin hukumar INEC zai shafi ingancin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel