Shugaban EFCC ya yi kakkausar gargadi ga jami’an hukumar

Shugaban EFCC ya yi kakkausar gargadi ga jami’an hukumar

  • Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya gargadi jami'an hukumar da ke aikata rashawa
  • Bawa ya shawarci bara-gurbin cikinsu da su yi murabus, inda yace babu yadda za a yi jami'in da ke aikata rashawa ya iya yakarta
  • Ya kuma sha alwashin cewa ba zai taba lamuntan kowani nau'i na rashawa ba a hukumar

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya nemi jami’ai “masu cin hanci” da ke cikin hukumar da su yi murabus.

Yayinda yake jawabi ga ma’aikatan EFCC reshen Markurdi, babban birnin jihar Benuwe, a ranar Alhamis, shugaban ya ce dole ne a kula da kimar aiki da mutunci yayin gudanar da aiki.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba a matsayin hutu

Shugaban EFCC ya yi kakkausan gargadi ga jami’an hukumar
Abdulrasheed Bawa ya bukaci jami'an EFCC da ke aikata rashawa da su yi murabus Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce ba zai yiwu jami'in da ke aikata cin hanci da rashawa ya yaki cin hanci da rashawa ba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

"Bari in tunatar da kowannenmu cewa muna yin aiki ne na musamman, cewa gwamnati, mutanen Najeriya da sauran kasashen duniya suna duba gare mu don samun ingantacciyar Najeriya," in ji shi.
“Ba za mu taba yarda da duk wani nau'i na rashawa a wannan wurin ba. Idan kai bara-gurbi ne, kana da 'yancin barin nan. Za mu yi farin cikin yin aiki tare da mutane kalilan, kuma a shirye muke mu yi kora. Idan kuna ganin ba za ku iya yin abin da dokokin kasa ke muradin mu yi ba, ku yi murabus ku bar mu mu kadai. ”

Ya bukaci ma’aikatan da su kasance masu himma da dabaru wajen tunkarar cin hanci da rashawa.

A cewarsa, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kan rantsuwarta, yayin da ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya ke duba zuwa gare ta don kawar da kasar daga cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Ya kuma ce hukumar za ta saka hannun jari a wajen bunkasa karfin dan Adam da horar da ma’aikata domin cimma manufarta, ya kara da cewa EFCC na aiki kan wasu tsare-tsare da za su bunkasa ci gabanta.

KU KARANTA KUMA: Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

“Muna gyara da kuma sake fasalin makarantar EFCC. Wannan don samun horar da ma’aikata da kyau ne don inganta aiki a yayin sauke hakokinmu don cimma burinmu da manufofinmu,” inji shi.

EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

A gefe guda, mun kawo cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta ƙaddamar da wata sabuwar manhaja da zata taimakawa yan Najeriya wajen tura rahoton aikata laifin cin hanci cikin sauƙi.

Shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa, wanda ya ƙaddamar da 'Manhajar Eagle Eye' a Abuja ranar Laraba, yace manhajar zata ba da damar ɗaukar hotuna da wuraren da ake zargin ana aikata laifuka, kamar yadda punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An damke Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD

Jim kaɗan bayan kammala taron, Bawa ya shaidawa BBC hausa cewa yunƙurinsu yana cikin shirin nan na fallasa bayanai da ake kira 'Whistle Blower'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng