Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

  • Bishop Kukah ya bayyanar da cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Buhari ba ta iya yin komi don magance matsalar tsaro
  • Ya ce gwamnati ce ta ‘yan uwa na addini da kabilar Shugaba Buhari
  • Ya yi zargin hare-haren da ake kai wa kan al’ummar Kiristoci ya karu a Arewa

Bishop na Katolika na yankin Sakkwato, Matthew Kukah, ya shaida wa Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka cewa Gwamnatin Tarayya ba ta iya yin komi game da matsalolin tsaro, wanda ta yi alkawarin magancewa kafin ta karbi mulki a 2015.

Ya fadi hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi game da yadda kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a Arewa ke muzgunawa Kiristoci a Najeriya, ga Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Tom Lantos da ke Washington, DC, a Amurka, rahoton Guardian.

Ya ce har yanzu mutane ba su ga wani kwakkwaran yunkuri na magance rashin tsaro ba, wanda a cewarsa, yana da nasaba da addini.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Kukah wanda Sakataren Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa ne ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da sanya ‘yan kabilarsa da addininsa a manyan mukaman siyasa da gangan.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba
Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD

Ya ce:

“Yankin Arewa, kai har ma da kasar baki daya, yan bindiga da masu satar mutane da sauransu, sun mamaye yankin da kasar.
“Lura da gwamnati kamar dai ba ta da gaske take yi ba ko kuma ba ta da sha'awar kawo karshen lamarin waɗannan mutanen yana kara rikita lamarin.
"Sabanin a nan shi ne cewa Shugaban kasa ya zabi fifita manufofi na siyasa ga wadanda yake addini da kaliba iri daya da su."

A cikin shaidar da ya gabatar a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Amurkar, mai rajin kare hakkin dan Adam din ya yi ikirarin cewa rikicin addini da ake yi kan Kiristoci a Najeriya ya kasance yana ta faruwa cikin tsawon shekaru, amma sannu a hankali yawan hare-haren ya karu a cikin shekara 10 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

A cewar Bishop din, masu tsattsauran ra'ayin sun fi maida hankali ne kan makarantun Kiristoci na Arewa, suna cusawa yara tunaninsu tare da maida 'yan matan zuwa matan aure da masu musu girki da leken asiri kwarkwarorinsu da dai sauransu.

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda rashin tsaro ke hana ci gaban kasar.

Jaridar The Nation ta ce Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata 13 ga watan Yuli yayin da yake karbar bakuncin sanatoci da mambobin majalisar wakilai a Abuja, babban birnin kasar.

Legit.ng ta ruwaito cewa Buhari ya ce matsalar tana tarnaki ga karfin gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa da kuma aiwatar da wasu manufofin ci gaba da gwamnatin ta sanya a gaba domin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel