Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP
- Jigon jam'iyyar APC a Zamfara, Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya yi kira ga Buni da IGP da su gaggauta tarwatsa bangaren Yari na jam'iyyar
- Kamar yadda Shinkafi ya sanar a wani koke da ya mika ga sifeta janar din, ya ce bangaren kullum burin shi tada tarzoma a jihar Zamfara
- Wannan ya biyo bayan kin yin mubaya'a da bangaren Yari yayi ga shugabancin Matawalle na jam'iyyar a jihar kamar yadda APC ta tanada
Zamfara
Wani jigo a jam'iyyar APC, Dr Sani Abdullahi Shinkafi yayi kira ga jam'iyyar da kuma sifeta janar na 'yan sandan Najeriya da su bada umarnin gaggauta tarwatsa sashin Abdulaziz Yari na APC a jihar Zamfara.
A wani korafi da aka mika ga sifeta janar na 'yan sandan Najeriya mai kwanan wata 15 ga Yuli, Shinkafi yace Yari da magoya bayansa suna kirkiro tashin hankali a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Muhuyi Rimingado
KU KARANTA: Mambobin APC sun farfashewa jami'in kotu baki a jihar Ogun
"Bayan sauya shekar da zababben gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad da ni muka yi daga jam'iyyar PDP da APGA zuwa APC, Gwamna Mai Mala Buni a jihar Yobe tare da kwamitinsa sun zo sun karbemu kuma sun sanar da rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar tun daga matakin jiha har zuwa guunduma.
"Gwamnan Buni ya baiwa Gwamnan Zamfara shugabancin jam'iyyar a jihar Zamfara. Washegarin gagarumin ralin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari wanda ya samu halartar gagarumin ralin yayi taro da nasa bangaren jam'iyyar a Kaduna inda ya karyata dukkan sanarwan shugaban jam'iyya na kasa," Shinkafi yace.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Yace daga faruwar wannan lamarin, Yari da magoya bayansa sun mayar da kansu masu tada zaune tsaye inda suke ikirarin tayar da tarzomar siyasa a jihar saboda wani ra'ayin son kansu da suke dashi kafin zuwa zaben 2023
A wani labari na daban, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rangwantawa talakawa. Basaraken yayi wannan kiran bayan karbar bakuncin shugaban kasan a fadarsa a ranar Alhamis.
Ya yi kira ga shugaban kasan da ya inganta tsaro tare da shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.
"Muna godiya ga shugaban kasa kan wannan ziyarar kuma hakan zai kara dankon alakarsa da gidan sarauta. Gidansa ne dama can. Ba za mu iya fadin sau nawa ya zo gidan ba ballantana a zamanin marigayin Sarki, a yayin shagali da babu," yace.
Asali: Legit.ng