Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

  • Gwamnatin Najeriya na shirin amfani da butumbutumi 'Robot' wajen yakar ta'addanci a kasar
  • Majalisar dattijai ne a Najeriya ta bayyana cewa, ma'aikatar sadarwa na aiki don tabbatar da shirin
  • Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, lamarin da ya kai ga lalata tattalin arzikin kasar

Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

KARANTA WANNAN: Korona: Gwamnati ta gargadi Musulman Najeriya game da yawon sallah da zuwa Idi

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Domin magance tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru
Shirin gwamnati na amfani da butumbutumi wajen yakar ta'addanci | Hoto: correctbn.com
Asali: UGC

Ministan Tsaro Ya Yi Sharhin Kalaman Buhari Na ‘Yaren da Suka Fi Fahimta’

Domin samar wa kasa mafita kan yawaitar ta'addanci, Shugaba Buhari ya caccaki masu tayar da kayar bawa, inda ya bukaci jami'an tsaro su yi kaca-kaca dasu kowa ma ya huta.

A cewar ministan tsaro Bashir Magashi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daidai da ya ce zai yi maganin masu aikata laifuffukan dake addabar kasar "da yaren da suke fahimta" .

A cewar ministan tsaron, babu wani aibi don shugaban kasar ya kawar da masu shirin hargitsa kasar, in ji jaridar Cable.

Magashi ya ce:

“Ba yadda za a yi ku mallaki makami ba bisa ka’ida ba kuma a bar ku ku rayu saboda ana iya amfani da makamin a kanku.
“Za mu dauki mataki kan duk wanda yake dauke da makamai. Najeriya ba za ta bari hakan ya ci gaba da faruwa ba. Wannan shine sakonmu.”

Kara karanta wannan

Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

Da yake ci gaba da bayani, ya sha alwashin cewa za a hukunta masu aikata laifuka a kasar nan domin doka za ta bi dasu yadda ya dace.

KARANTA WANNAN: An sanya dokar takaita zirga-zirga a Katsina saboda shugaba Buhari zai kai ziyara

Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

A wani labarin daban, A yammacin jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mambobin majalisar dokoki ta kasa, domin gudanar da wata liyafa.

Shugaban kasar ya tattauna da 'yan majalisu da sanatocin, yayin da ya bayyana wasu maganganu ciki har da yabo da ba da tabbaci da goyon baya a gwamnatinsa.

Hakazalika, jaridar Punch ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu ya bayyana matsalolin da kasar ke fuskanta, inda ya nemi goyon baya wajen magance su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel