Da Ɗuminsa: Gwamnan Kano Ganduje Ya Sake Yin Ƙarar Jaafar Jaafar a Kotu

Da Ɗuminsa: Gwamnan Kano Ganduje Ya Sake Yin Ƙarar Jaafar Jaafar a Kotu

  • Dr Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya sake yin karar Jaafar Jaafar da Daily Nigerian a kotu
  • Gwamnan na jihar Kano ya yi karar dan jaridan ne tare da Daily Nigerian kan zargin bata masa suna
  • An fara shari'a ne tsakanin Ganduje da Jaafar bayan dan jaridar ya fitar da fayafayen bidiyo aka ce gwamnan ne ke karbar daloli na cin hanci

Gwamnan jihar Kano, Abdulllahi Umar Ganduje ya sake yin karar Jaafar Jaafar da jaridar Daily Nigerian a wata babban kotun Abuja bisa zargin bata masa suna kamar yadda Daily NIgerian ta ruwaito.

A watan Oktoban 2018, jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a shafin intanet ta wallafa wasu fayafayen bidiyo da ke nuna gwamnan yana saka dalloli a aljihunsa da ake zargin cin hanci ne da dan kwangila ya bashi.

Da Ɗuminsa: Gwamnan Kano Ganduje Ya Sake Yin Ƙarar Jaafar Jaafar a Kotu
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da Mawallafin Daily Nigerian Jaafar Jaafar. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Bayan hakan, gwamnan ya yi karar mawallafin jaridar yana mai neman kotu ta tabbatar da cewa abinda Jaafar Jaafar da Daily Nigerian suka yi na 'wallafa maganganu da bidiyon karya a kafafen watsa labarai da cin mutunci da bata suna wanda ya shigar da karar laifi ne.'

Idan za a iya tunawa, babban kotu a jihar Kano, a ranar 6 ga watan Yuli ta umurci gwamnan Kano ya biya Daily Nigerian da mawallafinta N800,000 bayan ya yanke shawarar janye karar daga kotu.

A halin yanzu, akwai wata karar a kotu da aka shigar game da gwamnan na Kano inda dan jaridar ke neman a biya shi Naira miliyan 300 domin bata masa suna.

KU KARANTA: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A takardar kara mai dauke da kwanan wata na 15 ga watan Yuli da wakilin Daily Nigerian ya gani, kotun ta bukaci jaridar da mawallafinta su gabatar da takardar bawa lauya izinin ya wakilce su a kotu.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Takardar ta ce:

"Ana umurtar ka cikin kwanaki 14 bayan wannan takardar ka umurci a shigar da izinin a wakilce ka a karar da aka shigar kan Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yadda za a iya yanke hukunci koda baka nan."

Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara

A baya, wata babban kotun jihar Kano, a ranar Talata ta ci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tarar N800,000 bayan ya janye karar bata suna da ya shigar kan mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian, Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje ya maka mawallafin Ja'afar Ja'afar a kotu be saboda labari da bidiyon da ya wallafa inda aka gano wani da aka shine ke saka kudaden kasashen waje a cikin aljihunsa.

Kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Suleiman Danmallan, wadda ta amince da dakatar da shari'ar, ta umurci gwamnan ya biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa na jaridar N400,000 kowannensu.

Kara karanta wannan

An ba Dr. Abdullahi Ganduje kyauta a matsayin Gwamnan da ya yi fice a Jihohin Najeriya 36

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: