'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

  • Malamin addini mazaunin Sokoto Sheikh Bello Yabo ya umurci mutane su kashe mutumin da ake zargi da yi wa Annabi SAW batanci a Sokoto
  • Sheikh Yabo ya bayyana cewa ko da mutumin ya ce ya tuba hukuncin kisa na kansa a duniya idan ya tafi lahira Allah na iya masa gafara idan ya so
  • Sheikh Yabo ya bayyana cewa mutanen Sokoto ba kamar Kanawa bane da za su zauna suna jayayya idan har an samu wani da yi wa Annabi SAW batanci

Malamin addinin musulunci, Sheikh Bello Yabo, ya bada umurnin a kashe wani matashi da aka kama a Sokoto bisa zargin yin batanci ga Annabi Muhammad SAW, NewsWireNGR ta ruwaito.

A makon da ta gabata, mutane da dama sunyi zanga-zanga zuwa fadar sarkin musulmi a Sokoto suna neman a hukunta wanda ake zargin mai suna Isma'il Isah.

'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto
Sheikh Bello Yabo. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Kara karanta wannan

An Kama Mai Gadi Da Ya Haɗa Baki Da Wasu Domin Sace Manajan Bankin Da Ya Ke Aiki

Rahotanni sun bayyana cewa Isah ya yi wasu rubutun batanci a shafin dandalin sada zumunta na Facebook saboda ya gaza samun aiki a karamar hukuma a jihar ta Sokoto.

An kuma zarge shi da zagi wani jami'in gwamnati wanda ya yi zargin shine ya hana shi samun aikin gwamnati.

Da ya ke martani game da kama mutumin yayin wa'azinsa, Sheikh Bello Yabo ya ce duk wani musulmi da ya yi batanci ga Annabi dole a 'kashe shi' kamar yadda ya fada cikin faifan bidiyo da NewsWireNGR ta wallafa.

A jawabin da ya yi a cikin faifan bidiyon, Sheikh Yabo ya ce su a Sokoto ba za su amince da irin wannan shegantaka ba domin duk wanda ya yi wa Manzon Allah batanci hukuncinsa kisa ne.

Malamin ya ce wasu na cewa mutumin ba shi da hankali sai dai ya ce hakan ba dalili bane domin mara hankali bai san ya siya waya da data ya kuma shiga Facebook ya yi wa manzo batanci ba.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

KU KARANTA: Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Wani sashi cikin jawabin Sheikh Yabo ya ce:

"Da an sakai ku kashe shi, maganan bai da hankali bata taso ba, toh baida hankali duk baida wanda yaka zagi sai Manzon Allah, muma bamu da hankali idan an taba Annabi, don haka irin mu ba mu da hankali idan bai da, da an sakai ku kashe shi.
"Kuma ba shi kadai ba duk wanda ya taba Manzon Allah ku kashe shi, bai da hukunci, ko Bello Yabo bai taba Manzon Allah bai da hukucin sai kisa."

Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin

A baya, kun samu labarin cewa an dan samu tashin hankali a jihar Sokoto a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuli, bayan zanga-zanga ta barke a jihar kan zargin kalaman batanci ga Annabi.

Kara karanta wannan

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Masu zanga-zangar sun yi dafifi zuwa fadar Sarkin Musulmi, suna neman a hukunta wanda ake zargin, Isma’il Isah, Premium Times ta ruwaito.

Tambuwal a cikin wata sanarwa ta hannun kwamishinansa na yada labarai, Isah Galadanchi, ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na daukar matakan da suka dace don ganin an gurfanar da wanda ake zargin a gaban Shari’a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel