An ba Dr. Abdullahi Ganduje kyauta a matsayin Gwamnan da ya yi fice a Jihohin Najeriya 36
- Kungiyar ‘Yan jaridar Majalisar Tarayya ta ba Dr. Abdullahi Ganduje babbar kyauta
- Gwamnan ya yi fice wajen gyara harkar ilmi da samar da abubuwan more rayuwa
- Ganduje ya ce gwamnatin Kano ta maida karatun firamare zuwa sakandare kyauta
Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya yaba da kokarin gwamnatin mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
The Nation ta ce Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yabi gwamnan ne bayan ya yi zarra wajen bunkasa harkar ilmi da samar da abubuwan more rayuwa.
An ba Dr. Abdullahi Umar Ganduje wannan kyauta ne a wani biki da aka shirya a babban dakin taro na International Conference Centre da ke garin Abuja.
KU KARANTA: Gwamnan Legas ya damke masu yi wa motoci fashi a kan titi
A ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, 2021, aka shirya wannan biki da ya samu halartar gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar tarayya, jakadun waje da manyan kasa.
Kungiyar ‘yan jaridan majalisar tarayya ta ce ta yi bincike a kan tsare-tsaren ilmi a jihohi da yunkurin samar da abubuwan more rayuwa a jihohin Najeriya.
Binciken da aka gudanar ya nuna wa manema labaran cewa jihar da tayi zarra a wannan sahu ita ce Kano, a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Ganduje: Ka cancanci wannan lamba - Femi Gbajabiamila
Kamar yadda rahoton ya bayyana, shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila aka zaba domin ya mika wa gwamna Abdullahi Ganduje wannan kyauta.
KU KARANTA: Buhari ya karbi Gwamnonin da su ka shigo Jam'iyyar APC
“Ina taya ka murna. Ka dace kwarai da wannan (kyauta). Ina mai yabonka da jinjina maka.”
Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi godiya
Da ya karbi kyautar, Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi godiya da aka zabe shi, ya ce hakan zai kara masa kwarin gwiwar yi wa al’ummar jihar Kano aiki.
Gwamnan ya yi bayanin yadda ya maida ilmin firamare da sakandare ya zama kyauta a Kano, da irin kokarin da gwamnatinsa ta ke yi domin ta rikida jihar.
A baya an ji cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi ram da wasu da ake zargin suna aikata luwadi a wata unguwa da ke karamar hukumar Kumbotso.
An cafke mutanen har su biyar bayan samun rahoton zargin abubuwan da suke aikatawa a gari.
Asali: Legit.ng