Labari da dumi-dumi: Majalisa ta amince da rokon cin danyen bashin Naira Tiriliyan 4
- ‘Yan Majalisar Dattawa sun yi na’am da bukatar cin bashin Naira Tiriliyan 4
- Yau kwamitin Sanata Clifford Ordia ya gabatar da rahoton zaman da su ka yi
- An amince da rokon kwanaki bayan an yarda a ci bashin Naira tiriliyan 2.3
A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, 2021, majalisar dattawan Najeriya ta amince wa gwamnatin tarayya ta karbo aron bashin kudi daga kasar waje.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Sanatoci sun yarda a karbo fam Dala $8,325,526,537.0, da Euro miliyan €490, 000, 000 a matsayin bashin da za a ci.
Gwamnatin tarayya za ta yi amfani da wannan bashi ne domin ta cike gibin da aka samu a kasafin kudin shekarun 2018, da 2019, da 2020 da aka yi.
KU KARANTA: Majalisa ta amince Buhari ya karb bashin N850,000,000,000
Sanatoci sun amince da wannan rokon ne bayan shugaban kwamitin cin bashin gida na waje, Sanata Clifford Ordia ya gabatar da rahoton aikinsu.
The Nation ta tabbatar da rahoton dazu da rana, amma ba ta kawo cikakken bayanin wannan labari.
Me za ayi da wannan kudi?
A watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisa ta ba shi dama ya karbo aron wadannan kudi daga bankunan kasashen ketare.
Za a ci bashin ne daga bankuna da hukomomi da suka hada da bankin Duniya, bankin cigaban nahiyar Afrika, da bankin nan na cigaban kasar Faransa.
KU KARANTA: ‘Yan Majalisa su na binciken cin bashin da Najeriya ke yi
Najeriya za ta karbo aron wadannan kudi daga bankin cigaban musulunci, da bankunan China EXIMBank, wasu bankuna a kasar Sin da nahiyar Turai.
Gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kudin ne wajen yin ayyuka a wasu jihohin da ke kasar nan.
Ayyukan more rayuwan da za ayi za su shafi bangaren kiwon lafiya, harkar noma da abinci, ilmin boko da kuma bada tallafi a sakamakon annobar COVID-19.
Kwanakin baya kun ji cewa bashin da ke kan wuyan Najeriya ya haura Naira tiriliyan 30 a karshen watan Yunin bana, inji hukumar da ke kula da bashi.
Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbo aron Naira tiriliyan 18.89 a shekaru biyar.
Asali: Legit.ng