Korona: Gwamnati ta gargadi Musulman Najeriya game da yawon sallah da zuwa Idi

Korona: Gwamnati ta gargadi Musulman Najeriya game da yawon sallah da zuwa Idi

  • Cibiyar Kula da Cututtuka ta NCDC ta gargadi ilahirin musulmi kan yawaita tafiye-tafiya a lokacin sallah
  • Ta ce ya kamata mutane su kula duba da yadda aka samu bullar sabon nau'in Korona mai kisa a Najeriya
  • An bukaci masu ruwa da tsaki da malamai su ja hankulan mabiyansu tare da wayar musu kai kan Korona

Yayin da musulmai masu ke shirin bikin sallah babba a mako mai zuwa, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadi game da tafiye-tafiye a lokacin bukukuwan sallah.

Shugaban NCDC na Sashin Sadarwa, Dakta Yahya Disu, shi ne ya bayar da wannan gargadin a ranar Laraba yayin shirin karin kumallo na gidan Talabijin din Channels.

Disu ya ce karo na biyu na annobar Korona ta fara ne a Najeriya saboda mutane sun yi tafiya don Kirsimeti a Disambar da ta gabata. Don haka, ya bukaci 'yan Najeriya da su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci a lokacin bukukuwan sallah na mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

KARANTA WANNAN: Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Korona: NCDC ta gargadi Musulmai game da yawon babbar sallah
Shugaban cibiyar kula da cututtuka ta NCDC | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya bukaci shugabannin addinai da su wayar da kan mabiyansu a kan wajabcin kiyaye ka’idojin Korona domin kiyaye karuwar yaduwar cututtuka, Punch ta ruwaito.

Disu ya ce:

"Mafi mahimmanci, sallah tana zuwa, lokacine da mutane ke tafiye-tafiye kuma hakan na kara hadari ga kauyuka, a sassa daban-daban na kasar.

"Don haka, muna bukatar fadakar da mutane: ba sa bukatar tafiye-tafiye idan ba dole ba ne, za ku iya yin biki a inda kuke. A lokacin sallah, muna zuwa masallaci adadi mai yawa kuma wannan shine lokacin da ya kamata mu kiyaye.

An samu bullar sabon nau'in Korona karo na uku

A baya an bayar da rahoton cewa da aka gano sabon nau'in Korona a Deltat a Najeriya, masana sun yi gargadi game da sake sanya dokat kulle, suna masu cewa sanya sabon kullen na da matukar illa ga tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

Kwararrun sun yi magana game da asalin nau'in Korona karo na uku tare da ci gaba da samun karuwar masu dauke da cutar cikin makon da ya gabata da kuma gano wani sabon nau'in kwayar cutar a Najeriya.

Nau'in na Korona ta Delta wacce Kungiyar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da samuwarta an ce tana saurin kisa saboda yadda take saurin yaduwa, kamar yadda cibiyar NCDC ta tabbatar, The Guardian ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Wata sabuwa: Ana kyautata zaton dage sauraran shariar Nnamdi Kanu saboda wasu dalilai

Shugaba Buhari ya karbi allurar rigakafin korona kashi na biyu

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi allurarsa ta rigafin korona wato AstraZeneca COVID-19 kashi na biyu.

Shugaban kasar ya karbi allurar ne a gidansa da ke fadar Shugaban kasa, Abuja, a yau Asabar, 29 ga watan Mayu.

Fadar Shugaban kasar c eta tabbatar da hakan a wani wallafa da tayi a shafinta na Twitter. Anyi kashi na biyun ne makonni 12 cif bayan ɗaukar farko a ranar 6 ga Maris.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.