An sanya dokar takaita zirga-zirga a Katsina saboda shugaba Buhari zai kai ziyara

An sanya dokar takaita zirga-zirga a Katsina saboda shugaba Buhari zai kai ziyara

  • Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Katsina domin kaddamar wasu ayyuka a jihar gobe Alhamis
  • Rahoto ya bayyana cewa, a halin yanzu an fara rufe hanyoyi a fadin jihar domin jiran isowar Buhari
  • Rundunar 'yan sanda ta fara gudanar da aikin rufe hanyoyi domin tabbatar da tsaro a fadin jihar

A ranar Laraba ne rundunar ‘yan sanda ta Katsina ta sanar da rufe wasu manyan hanyoyi a cikin jihar a matsayin wasu matakan tsaro na ziyarar Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

Manyan titunan da abin ya shafa sune Dutsinma zuwa Kankara da Dutsinma zuwa Tsaskiya.

Hakanan kuma za a rufe hanyoyi masu hade da musu a fadin yankin, Punch ta ruwaito.

Rufewar zai kasance daga 1 na yamma zuwa 6 yamma a ranar alhamis.

KARANTA WANNAN: Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari zai je ziyara jihar Katsina, an fara rufe hanyoyi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Depositphotos

An takaita zirga-zirga saboda zuwan shugaba Buhari

Rundunar ta kuma sanar da takaita zirga-zirgar matafiya, masu tuka keke da makiyaya a lokacin ziyarar.

Ana sa ran Shugaban zai je jihar a ranar Alhamis don bude aikin samar da ruwa na yankin Zobe da hanyar Tsaskiya.

Hanyoyin da za rufen suna daga cikin garuruwan dake da ayyuka biyu da za a kaddamar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isah, ya fitar a Katsina ranar Laraba, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito, ya ce:

“Rundunar‘ 'yan sanda ta jihar Katsina na son sanar da jama’a cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, zai iso Katsina a ranar 15 ga Yuli, 2021 don kaddamar da Aikin samar da Ruwa na Yanki a Zobe da kuma sabon titin Tsaskiya, karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
“Bisa la’akari da abin da ke sama, rundunar tana son sanar da rufe hanyar Dutsinma-Kankara, hanyar Dutsinma-Tsaskiya da sauran hanyoyin da ke kusa da inda za a gudanar da taron a ranar 15 ga Yuli, 2021 daga 13: 00hrs - 18: 00hrs.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

“An umarci jama’a, musamman matafiya, makiyaya, masu tafiya a kafa da masu keke cewa su yi amfani da wasu hanyoyi."

KARANTA WANNAN: Korona: NCDC ta gargadi Musulmai game da yawon babbar sallah, ta fadi sharudda yawo

Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

A wani labarin, A yammacin jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mambobin majalisar dokoki ta kasa, domin gudanar da wata liyafa.

Shugaban kasar ya tattauna da 'yan majalisu da sanatocin, yayin da ya bayyana wasu maganganu ciki har da yabo da ba da tabbaci da goyon baya a gwamnatinsa.

Hakazalika, jaridar Punch ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu ya bayyana matsalolin da kasar ke fuskanta, inda ya nemi goyon baya wajen magance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel