Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama

Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama

  • Rikici ya barke tsakanin 'yan kasuwa a jihar Legas da sojoji tare da 'yan daba a fitacciyar kasuwar Ladipo
  • Sai dai an gano 'yan kasuwa uku sun sheka lahira yayin arangamar da ta hada da 'yan daba a yankin
  • Har a halin yanzu ba a san dalilin wannan rikicin ba amma sojoji da 'yan sandan kwantar da tarzoma sun isa wurin

'Yan kasuwa uku ne aka gano sun rasa rayukansu sakamakon arangamar da ta auku tsakaninsu da jami'an rundunar sojin sama da 'yan daba a Legas.

Har ila yau, Daily Trust ta ruwaito cewa wasu jama'a da dama sun samu miyagun raunika a fito na fito da aka yi a fitacciyar kasuwa Ladipo dake Mushin, Legas a ranar Talata.

KU KARANTA: Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa

Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama
Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sunaye: Gimbiya da dan shekara 1 daga cikin iyalin sarkin Kajuru dake hannun 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Rikicin ya tirsasa 'yan kasuwa a kasuwar rufe kasuwancinsu domin gujewa abinda zai kai ya kawo.

Har yanzu ba za a ce ga dalilin da ya kawo rigimar ba a yayin rubuta wannan rahoton, Daily Trust ta wallafa hakan.

Sai dai majiyoyi sun tabbatar da cewa tawagar sojoji da 'yan sandan kwantar da tarzoma tuni suka isa wurin domin kwantar da tashin hankalin.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi bai amsa kiran da aka dinga yi masa ba tare da sakon da aka aika masa da shi.

Hakazalika, an dinga kira layin kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, amma ba a samunsa.

A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara

An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel