Da Duminsa: JAMB ya fitar da sakamakon jarrabawar 'mock' na 2021

Da Duminsa: JAMB ya fitar da sakamakon jarrabawar 'mock' na 2021

  • Hukumar Jamb ya fitar da sakamakon jarrabawar gwaji da aka yi a watan Yuni
  • Hukumar ta ce mutum 160,718 ne suka nuna sha'awar rubutawa amma 62,780 ne suka rubuta
  • Jamb ta ce duk wanda ke son duba sakamakon jarrabawar ya tafi shafinta na www.jamb.gov.ng

Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare a Nigeria, JAMB, ya fitar da sakamakon jarrabawar gwaji da ake kira 'mock' wanda aka a rubuta a ranar 3 ga watan Yunin 2021, The Punch ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar JAMB, Dr Fabian Banjamin ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Dalibai na rubuta jarrabawa
Dalibai yayin rubuta jarrabawa. Hoto: PM News
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

Kakakin na Jamb ya ce:

"Sakamakon jarrabawar gwaji ta mock da muka yi a ranar 3 ga watan Yuni yana nan a shafinmu na intanet.
"Wadanda suka rubuta jarrabawar suna iya duba sakamakonsu a www.jamb.gov.ng (ka latsa shafin sannan ka shigar da bayannan ka da lambar rajista domin ganin sakamakon).
"Jimillar mutane 160,718 ne suka cike bayanai cewa za su rubuta jarrabawar amma cikinsu 62,780 ne kadai suka rubuta jarrabawar da a yanzu aka fitar da sakamakon."

DUBA WANNAN: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta ruwaito cewa za a rubuta ainihin jarrabawar ta Jamb daga ranar 19 ga watan Yuni zuwa 3 ga watan Yulin shekarar 2021.

Jamb ba ta bada kididdigan wadanda suka yi nasarar a jarrabawar ba.

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel