Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

  • Gandireba ya bindige wani mutum da ya zo ziyarar abokinsa a gidan gyaran hali a jihar Delta
  • An bindige mutumin ne bayan an gano hodar iblis cikin kayan da ya zo da su kuma ya yi yunkurin tserewa
  • Wani da abin ya faru a gabansa ya ce da farko gandireban ya harbi mutumin a kafa sannan ya sake harbinsa ya mutu nan take

Wani jami'in tsaro a gidan gyaran hali na Okere a jihar Delta ya bindige wani mutum da ya ziyarci abokinsa a gidan gyaran hali da ke Okere jihar Delta, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Jami'in tsaron ya harbi mutumin sau biyu hakan ya yi sanadin rasuwarsa a cewar majiyar da ya shaidawa SaharaReporters game da afkuwar lamarin a ranar Talata.

Gidan Yarin Okere, Jihar Delta.
Gidan Gyaran Hali na Okere a Jihar Delta. Hoto: Linda Ikeji
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

Linda Ikeji ya ruwaito cewa an ce mutumin ya ziyarci abokinsa ne da ke gidan gyaran halin inda ya kai masa tumaturi da wasu kayayakin abinci.

Amma jami'an tsaron na gidan yari sun gano hodar iblis wato koken a cikin kayan abincin.

A cewar majiyar, an kama mutum an masa tambayoyi amma ya gamu da ajalinsa a lokacin da ya yi yunkurin tserewa.

An gano cewa jami'in tsaron ya harbe shi a kafa ne a lokacin da ya ke kokarin tserewa sannan ya sake harbinsa a lokacin da ya ke rarafe yana fama da azabar harbin bindigan.

KU KARANTA: 'Yan bindige sun bi manajan 'stadium' har wurin aiki sun bindige shi har lahira a Jos

Labarin mutuwar matashin ya jefa mutanen garin cikin firgici a yayin da matasa suka fito suna zanga-zanga.

"Mutane na cikin firgici a gidan yarin Okere a Warri a yayin da gandireba ya harbe wani wanda ya kawo ziyara a yau da rana. An ce bakon ya zo ya ga abokinsa ne a lokacin da abin ya faru.

"Abin da mutane a waje suka gani mutumin ya zo da tumatur da wasu kayan abinci. Da ake bincike sai aka gano hodar koken da wasu kaya. Daga nan aka masa tambayoyi," in ji majiyar.

Amma da ya ga alamar yana cikin matsala, sai ya fara gudu. Daya daga cikin gandirebobin ya harbe shi a kafa. Yana cigaba da rarafe, sai ya sake harbinsa ya mutu," a cewar majiyar.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel