An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

Hukumar NSCDC ta yi nasarar kama wata Omolara Slanke da ta damfari wani dan siyasa kudi N2.6m

Solanke da wasu mutane biyar sun tafi da wanda aka damfara wani gari a Ekiti sannan suka kwace kudin suka tsere

Hakan yasa dan siyasar ya shigar da kara ofishin hukumar NSCDC inda nan take aka fara bincike kuma aka gano Solanke

Hukumar tsaro ta NSCDC, jihar Osun, a ranar Talata ta ce ta kama wata Omolara Solanke da ake zargi da karbar kudi N2,680,000.000 daga hannun wani mai rike da mukamin siyasa ta hanyar yaudararsa, The Punch ta ruwaito.

Kakakin NSCDC a jihar, Daniel Adigun, cikin wata sanarwa, ya yi bayanin cewa wanda ake zargin an dauke ta aiki ne ta taimakawa wani dan siyasa, Razaq Salami, mai shekaru 48, ya ci zaben kansila.

Taswirar Nigeria
Taswirar Nigeria yana nuna jihar Osun. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewar matar ta yi wa dan siyasar alkawarin cewa za a yi amfani da 'iskokai' ne domin a taimaka masa ya lashe zaben.

DUBA WANNAN: Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

Ya kamata a yi amfani da kudin ne domin biyan wacce ake zargin yar shekara 46.

Adigun ya ce wacce ake zargin tare da wasu mutane biyar sun kai wanda abin ya faru da shi wani gari a jihar Ekiti inda suka karbi kudin daga hannunsa sannan suka tsere.

"Bayan ya yi kokarin tuntubar yan dafarar amma bai yi nasara ba, Razaq ya shigar da kara a ofishin NSCDC a sashin masu yaki da yan damfara inda nan take aka fara bincike. NSCDC na jihar Osun ta yi nasarar gano yan damfarar.

KU KARANTA: 'Yan bindige sun bi manajan 'stadium' har wurin aiki sun bindige shi har lahira a Jos

"A yayin binciken, an kamo Omolara Solanke. Shugaban NSCDC na jihar Osun ta hannun sashin yaki da masu damfara ya mika wanda ake zargin ga rundunar NSCDC ta jihar Ekiti don cigaba da bincike da gurfanarwa," a cewar sanarwar.

A wani rahoton, Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel