Gwamnatin Gombe ta nada Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon sarkin Funakaye

Gwamnatin Gombe ta nada Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon sarkin Funakaye

- Gwamnan jihar Gombe ya amince da nadin Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga, a matsayin sabon sarkin masarautar Funakaye

- Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo Waziri

- Nadin nasa na zuwa makonni biyu bayan mutuwar mai martaba tsohon sarkin Funakaye, Alhaji Muhammadu Kwairanga Abubakar II

Gwamnatin Gombe ya yi na’am da nadin Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga, Dan majen Funakaye a matsayin sabon sarkin masarautar Funakaye.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an sanar da nadin sabon sarkin ne a wata takarda dauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, zuwa ga manema labarai a ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Matawalle ya ba Zamfarawa wa'adin kwana 7 su mika makaman da suka mallaka

Gwamnatin Gombe ta nada Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon sarkin Funakaye
Gwamnatin Gombe ta nada Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon sarkin Funakaye Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Takardar ta bayyana cewa nadin nasa ya biyo bayan dokar da ta baiwa Gwamna damar nadawa tare da tsige sarki bisa amincewar masu zabarsa da shawarwari daga kwararru.

Hakazalika da yake mika wa sabon sarkin takardar nadin nasa a fadar sarki da ke garin Bajoga na karamar hukumar Funakaye, kwamishinan ya bukace shi da ya riki kowa a matsayinsa na uban kasa.

Ya kuma bayyana wa sarkin cewa nan ba da jimawa ba za a yi bikin wankan sarauta da kuma mika masa sandar girma.

Sabon sarkin ya kasance kani ga marigayi tsohon sarki Muhammad Kwairanga Abubakar, wanda ya rasu makonni biyu da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: JTF ta kama mutum 10 da ake zargi da kisan jami'an tsaro a Akwa Ibom, an samu miyagun makamai

Kafin nadin nasa, shine ke rike da sarautar Dan Majen Funakaye.

A baya Legit.ng ta kawo cewa Mai martaba sarkin Funakaye a jihar Gombe Alhaji Muhammadu Kwairanga Abubakar II ya riga mu gidan gaskiya.

Sarkin ya rasu ne a safiyar Alhamis, 20 ga watan Mayu, a Bajoga kamar yadda BBC ta ruwaito. Ya rasu yana da shekaru 68 a duniya.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan sarkin da al'ummar masarautar da ma kasa baki daya bisa wannan babban rashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel