JTF ta kama mutum 10 da ake zargi da kisan jami'an tsaro a Akwa Ibom, an samu miyagun makamai
- Jami'an tsaron hadin guiwa a jihar Akwa Ibom sun cafke wasu mutum 10 da ake zargi da kaiwa jami'an tsaro farmaki
- Rundunar hadin guiwan ta JTF ta hada da sojoji, 'yan sanda, jami'an hukumar tsaron farin kaya da kuma na NSCDC
- JTF sun kai samame lunguna da sakonni na jihar inda suka damkesu tare da samun ababen hawa da miyagun makamai
Jami'an tsaron hadin guiwa (JTF) sun damke jama'a masu yawa masu alaka da kashe-kashen jami'an tsaro a kananan hukumomin Essien udim, Oboto Akara da Ikot Ekpene dake jihar Akwa Ibom.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, kamen ya biyo bayan jerin samamen da JTF din da suka hada sojoji, 'yan sanda, jami'an DSS da na NSCDC ke kaiwa wurare daban-daban da suka zama maboyar 'yan ta'adda a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Andrew Amiengheme, a wata takardar da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa JTF din sun samo ababen hawa da makamai daga wadanda ake zargin.
KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kori basarake daga fadarsa bayan mutuwar dan sanda a yankin
KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, kwamishinan 'yan sandan yace: "Idan zamu tuna a cikin kwanakin nan, an dinga samun jerin hare-hare ga jami'an tsaro da sansaninsu ballantana 'yan sanda. Lamarin da ya dinga kawo asarar rayuka da dukiyoyi.
"Bayan shiryayyun samame zuwa wurare daban-daban na 'yan ta'adda a Ntak Ikot Akpan, Abama da Ikot Akpan dake kananan hukumomin Essien Udim, Obot Akara da Iko Ekpene da jami'an hadin guiwa suka yi, an kama mutum 10 da ake zargin suna da alaka kai tsaye da kashe-kashen jami'an tsaro da salwantar da dukiyoyin jama'a.
“Wannan mummunan lamarin ne ya janyo dole aka kafa rundunar tsaro ta hadin guiwa wacce ta kunshi sojoji, 'yan sanda, jami'an DSS da na NSCDC. Aikin jami'an hadin guiwan ya haifar da da mai ido inda aka samu nasarori masu tarin yawa."
A wani labari na daban, kungiyar 'yan bindiga da suka shirya sace 'yan matan makarantar sakandare ta Jangebe dake jihar Zamfara a farkon shekarar nan, sune ke da alhakin kwashe daliban Islamiyya a Tegina dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, Daily Trust ta tabbatar.
Mambobin kungiyar sun kwashe dalibai masu yawa daga jihar Neja a ranar Asabar da ta gabata, wata majiya mai karfi ta tsaro ta sanar da Daily Trust, duk da babu dalilin wannan aika-aikar har yanzu.
Gagararriyar kungiyar 'yan bindigan da ta samu jagorancin Na-Sanda, sun dade suna ta'asa a dajin Jangebe dake karamar hukumarr Talatan Mafara ta jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng