Mun shirya tsaf don fito-na-fito da Buhari, Marasa rinjaye a majalisar dokoki

Mun shirya tsaf don fito-na-fito da Buhari, Marasa rinjaye a majalisar dokoki

Marasa rinjaye a majalisar dokokin tarayya a ranar Talata, sun yi gargadin yin amfani da karfinsu wajen fito-na-fito da shugaba Muhammadu Buhari idan ya cigaba da saba kundin tsarin mulki.

Gamayyar marasa rinjayen sun lissafa jerin laifukan da Buhari yayi wanda za su iya amfani da su wajen tsigeshi.

Jagoran gamayyar kuma shugaban marasa rinjayen majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe, ya bayyana hakan a hira da manema labarai ranar Talata, a Abuja, Punch ta ruwaito.

A cewarsa, gamayyar na matukar fushi da Buhari bisa gazawarsa wajen baiwa yan Najeriya ingantaccen tsaro, wanda shine babban amfanin gwamnati.

Hakazalika ya yi alhinin yadda tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare karkashin Buhari. A cewarsa, ba zai yiwu a cigaba da zama haka ba.

DUBA NAN: El-Rufa’i Ya Bayyana Yadda Alaƙarsa Tayi Tsami da Jonathan a Mulkinsa, Yace Ya Kusa Tura Shi Gidan Gyaran Hali

Mun shirya tsaf don fito-na-fito da Buhari, Marasa rinjaye a majalisar dokoki
Mun shirya tsaf don fito-na-fito da Buhari, Marasa rinjaye a majalisar dokoki Credit: @NGRSenate
Asali: UGC

KU DUBA: Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi

Yace, "Gamayyar ta lura kuma za ta cigaba da rubuta laifukan sabawa dokokin da gwamnatin APC ke yi."

"Idan lokaci ya yi zamuyi amfani da hanyoyin da doka ta tanada bayan tattaunawa da abokanmu domin yin abinda ya dace don ceto kasar nan daga rugujewa."

"Abin takaicin shine, daga 2015 zuwa yanzu, maimakon magance matsalar tsaro, gwamnatin APC ta kara tsananta matsalar ne."

"Daga matsalar Arewa maso gabas, abin ya yadu zuwa dukkan sassan kasar nan. Kusan kowani yanki a Najeriya yanzu na fama da wani matsalar tsaro."

Asali: Legit.ng

Online view pixel