Rashin Tsaro: Ya kamata Buhari Yayi Murabus Saboda Ya Gaza - Matasan Arewa
- Kungiyar matasan Arewa sun goyi bayan kira da ake na Shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus
- A cewar kungiyar, gwamnatin Buhari ta gaza ta bangaren tsaro da habbaka tattalin arziki
- Shugaban kungiyar, Danjuma Sarki ya ce hatta ga magoya bayan shugaban kasar sun juya masa baya saboda gazawarsa
Kungiyar matasan Arewa mai suna Arewa Youths for Progress and Development (AYPD) ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus saboda gazawar gwamnatin sa na magance rashin tsaro da tattalin arzikin da ke durkushewa.
Shugaban AYPD, Danjuma Sarki, ya bayyana cewa da wannan halin da kasar ke ciki a yanzu, gwamnatin Buhari ta gaza kuma ba za ta iya magance hauhawan matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ba.
KU KARANTA KUMA: Ku Bayyana Masu Kitsa Kifar da Gwamnatinku, Dattawan Arewa Ga Gwamnatin Buhari
Sarki ya goyi bayan faston Katolika, Fr. Ejike Mbaka, da sauran masu goyon bayan Buhari, wadanda suka yi kira ga Shugaban kasar ya yi murabus.
KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Atiku Ya Ba da Mafita Don Yakar ’Yan Fashi da Masu Tayar da Kayar Baya
Shugaban matasan ya ce: "A bayyane yake cewa Buhari ya gaza wajen jagorantar al'umma kan tafarkin ci gaban zamantakewa, siyasa da tattalin arziki. Abu mafi kyawu a gareshi shi ne yin murabus cikin girmamawa a matsayinsa na Shugaban kasa don tseratar da al'umma daga rugujewa da rikici.
“Matakan rashin tsaro a kasar na karuwa a kullum. ‘Yan Boko Haram suna kashe‘ yan Najeriya a arewa; akwai sace-sacen mutane a duk fadin kasar da kashe-kashen da ‘yan fashi da makami ke yi, kuma gwamnati ba ta samar da hanyar magance dukkan rikice-rikicen ba. Shin ta haka ne za'a gudanar da mulkin kasar a karkashin wannan barazanar, kuma 'yan Najeriya su dunga rayuwa cikin tsoro? "
Ya lura cewa hatta tsofaffin mabiyan Buhari sun ja da baya daga mara masa baya tare da neman Buhari ya yi murabus.
“Gwamnati ta gaza matuka saboda haka ya kamata Shugaban kasa ya yi murabus yanzu. A bar shi ya tafi. Yakamata ya ceci Najeriya. Matakin kashe-kashe da satar mutane ya wuce gona da iri, ”ya kara da cewa.
A wani labarin, Primate Elijah Ayodele, Shugaban Cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya bayyana cewa ba za a tsige Shugaba Muhammadu Buhari daga ofishin sa ba.
Ya ba da tabbacin cewa duk da cewa mulkin Buhari zai fuskanci cin hanci da rashawa, rudani, babu wani juyin mulki da za a yi mashi, PM News ta ruwaito.
Martanin nasa ya biyo bayan gargadin da fadar shugaban kasa ta yi cewa wasu ‘yan kasar na shirin kwace gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng