Gurfanar da Masu Satar Mutane, Yan Bindiga a Gaban Kotu Ba Aikin FG Bane, Lai Muhammed

Gurfanar da Masu Satar Mutane, Yan Bindiga a Gaban Kotu Ba Aikin FG Bane, Lai Muhammed

- Ministan yaɗa labarai da raya al'adu na ƙasa, Alhaji Lai Muhammed, ya maida martani kan Zargin da babbar jam'iyyar hamayya PDP tayiwa gwamnatin tarayya

- PDP dai tayi zargin cewa gwamnatin tarayya ba ta gurfanar da yan bindiga da masu satar mutane a gaban kotu don a hukunta su

- Ministan yace wannan ba ƙaramin abun mamaki bane ace jam'iyyar da ta mulki ƙasar nan na tsawon shekara 16 bata san laifukan tarayya da na jihohi ba

Ministan yaɗa labarai da raya al'adu, Alhaji Lai Muhammed, a ranar Talata yace aikin gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata satar mutane, da yan bindiga bana gwamnatin tarayya bane.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah

Ministan yace laifin satar mutane da kuma na yan bindiga ba laifuffukan tarayya bane, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Minista Lai Muhammed ya faɗi haka ne a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Gurfanar da Masu Satar Mutane, Yan Bindiga a Gaban Kotu Ba Aikin FG Bane, Lai Muhammed
Gurfanar da Masu Satar Mutane, Yan Bindiga a Gaban Kotu Ba Aikin FG Bane, Lai Muhammed Hoto: fmic.gov.ng
Asali: UGC

Ya faɗi hakane yayin da yake martani a kan wani jawabi da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP tayi game da ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fama dashi.

Ministan yace:

"Jam'iyyar PDP tayi zargin cewa masu satar mutane, da yan bindiga ba'a gurfanar dasu a gaban alƙali. Wannan a bayyane yake ana zargin gwamnatin tarayya da wata manufa ne ta daban."

KARANTA ANAN: Ku Ƙara mana Lokaci kar ku kashe 'yayan mu, Iyayen Ɗalibai sun Roƙi yan Bindiga

"Abun mamaki ne matuƙa ace jam'iyyar data mulki ƙasar nan na tsawon shekaru 16 bata san cewa laifukan satar mutane da na yan bindiga ba laifukan tarayya bane."

"Saboda haka, kamata yayi jam'iyyar PDP ta kira gwamnatocin jihohi harda waɗanda ita ke rike dasu, domin su tabbatar an gurfanar da waɗanda aka kama da zargin aikata satar mutane ko yan bindiga ta hanyar data dace."

Daga ƙarshe, ministan yace:

"Da alama PDP ta manta cewa aikin ta'addanci, wanda laifin tarayya ne, gwamnatin tarayya ta gurfanar da dubban Mambobin ƙungiyar Boko Haram a gaban kotu."

"A yanzu muna buƙatar haɗin kan alƙalai da kotu domin a cigaba da shari'a a kan yan ta'addan da aka kama."

A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani

Ministan Shari'a kuma Antoni Janar (AGF) na ƙasar nan , Abubakar Malami, ya bayyana dalilin da yasa aka samu tsaiko wajen dawo da kuɗaɗen da Ibori ya sace.

Kakakin AGF ɗin, Dr. Umar Gwandu, ya faɗi cewa wasu takardun banki ne suka ɗauki tsawon lokacin da ba'a yi tsammani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel