Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani

Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani

- Ministan Shari'a kuma Antoni Janar (AGF) na ƙasar nan, Abubakar Malami, ya bayyana dalilin da yasa aka samu tsaiko wajen dawo da kuɗaɗen da Ibori ya sace

- Kakakin AGF ɗin, Dr. Umar Gwandu, ya faɗi cewa wasu takardun banki ne suka ɗauki tsawon lokacin da ba'a yi tsammani ba

- Sai dai ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya na aiki tuƙuru wajen ganin an dawo da kuɗin cikin nasara ba tare da samun wata matsala ba

Antoni Janar na ƙasar nan (AGF) kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, yayi bayanin dalilin da yasa aka samu tsaiko a dawo da £4.2 miliyan da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ya sace.

KARANTA ANAN: Yan Najeriya Zasu Sami Kwanciyar Hankali a Mulkin Buhari, Bola Tinubu

A wani taro ranar 9 ga watan Maris, Malami, wanda ya wakilci gwamnatin tarayya ya sanya hannu kan yarjejeniyar dawo da kuɗin da Catriona Laing, kwamishinar Burtaniya a Najeriya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani
Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani Hoto: @MalamiSan
Asali: Twitter

A wajen taron, an sanar da cewa za'a dawo da kuɗaɗen cikin makwanni biyu daga ranar da aka sanya hannu kan yarjejeniyar.

A wani jawabi da kakakin AGF, Dr Umar Gwandu, ya fitar ranar Litinin yace an samu tsaikon ne saboda ɗaukar lokaci da takardun banki suka ɗauka wanda ba'ayi tsammanin faruwar hakan ba.

Sai-dai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana domin ganin an dawo da kuɗaɗen Najeriya da aka sace kuma aka ajiye su a wasu kasashen waje.

KARANTA ANAN: Yan Najeriya Zasu Sami Kwanciyar Hankali a Mulkin Buhari, Bola Tinubu

Yace: "Takardun yarjejeniyar dawo da kuɗin na wasu bankunan ƙasashe daban-daban ne suke ɗaukar lokacin da ba'ayi tsammani ba. Munyi tsammanin za'a kammala komai cikin makwanni biyu amma bamu keda iko da bankunan ba."

"Duk wani ƙoƙari da gwamnati zatayi ta riga tayi domin ganin kuɗin sun dawo cikin nasara ba tare da samun wata matsala ba."

Sai dai tun a kwanakin baya, Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa zata yi amfani da kuɗaɗen wajen kammala wasu muhimman ayyuka da ake tsaka da yinsu kamar; Gadar Neja ta biyu, babbar hanyar Abuja zuwa Kano, da kuma hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Amma wannan sanarwar ta gwamnatin tarayya ta jawo cece-kuce, yayin da gwamnatin jihar Delta da wasu sanannun Lauyoyi suka buƙaci a maida kuɗin jihar Delta.

A wani labarin kuma Minista Ya Bayyana Matakin da Yakamata a Ɗauka Kan Gwamnonin da Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashi

Ministan ƙwadugon ƙasar nan , Dr. Chris Ngige, yace duk wani gwamna da ya kasa biyan mafi ƙarancin albashi to ya sani ya karya dokar ƙasa.

Ministan yayi wannan jawabi ne yayin da yake zantawa a cikin wani shirin kafar yaɗa labarai, yace dokar tace wajibine a biya ma'aikaci mafi ƙarancin Albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262