Kaico: Wasu yan bindiga sun sheƙe wani malamin coci a jihar Benue

Kaico: Wasu yan bindiga sun sheƙe wani malamin coci a jihar Benue

- Wasu yan bindiga sun hallaka faston wata cocin katolika dake ƙaramar hukumar Katsina-Ala, jihar Benue

- Yan bindigan sun kai hari ne a harabar cocin katolika Inda suka hallaka fasto da kuma wasu mutane su uku

- Sai dai hukumar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin amma tace malamin cocin ne kaɗai aka kashe har lahira

An kashe wani malamin ɗariƙar katolika, Ferdinand Fanen Ngugban, a yankin karamar hukumar Katsina-Ala, jihar Benue.

KARANTA ANAN: Kuskuren harshe ne ba haka naso fada ba, Tinubu ya gyara kalamansa kan ɗaukar matasa aikin soja

Jaridar Dailytrust ta gano cewa wasu yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba sune suka hallaka malamin kuma suka cinna ma wasu gidaje wuta.

Yan bindigan sun yi wannan aika-aikan ya yin da suka farmaki garin ba zato ba tsammani, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Shugaban yankin na Kastina-Ala, Joseph Atera, ya shaidama wakilin Dailytrust cewa yan bindigan sun kaima rabaran ɗin hari ne a harabar cocin, kuma sun kashe wasu mutane uku daban.

Kaico: Wasu yan bindiga sun sheƙe wani malamin coci a jihar Benue
Kaico: Wasu yan bindiga sun sheƙe wani malamin coci a jihar Benue Hoto: @Daily_trust
Source: Twitter

Amma jami'i mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da kisan malamin cocin ne kaɗai banda sauran mutanen.

KARANTA ANAN: Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista

"Tabbas ankai hari cocin katolika dake ƙauyen Aye-Twar ƙaramar hukumar Katsina-Ala, kuma sanadiyyar wannan harin aka kashe rabaran ɗin cocin." inji shi.

Haka zalika, Mai magana da yawun yan sandan ya bayyana cewa an kai gawar wanda ya rasa rayuwarsa zuwa wurin adana gawa dake babban asibitin garin Katsina-Ala.

Ya kuma ƙara da cewa jami'an yan sanda tare ɗa haɗin guiwar wasu hukumomin tsaro sun bazama neman waɗan da suka aikata wannan aika-aika.

A wani labarin kuma Barayi Sun Yi Wa Beyonce Satar Kayayyakin Da Kuɗinsu Ya Kai Dala Miliyan Ɗaya

Barayi sun yi wa fitacciyar mawakiya Giselle Knowles-Carter, mai yara uku, satar kayayyaki masu daraja da kudinsu ya kai Dallar Amurka miliyan daya,.

Rahotanni sun ce yan fashin sun sace jakunkuna da tufafi da kudinsu ya fi dalla miliyan daya.

Source: Legit.ng

Online view pixel