Kuskuren harshe ne ba haka naso fada ba, Tinubu ya gyara kalamansa kan ɗaukar matasa aikin soja

Kuskuren harshe ne ba haka naso fada ba, Tinubu ya gyara kalamansa kan ɗaukar matasa aikin soja

- Jagoran jam'iyyar APC Bola Tinubu ya bayyana cewa shifa ba yana nufin gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja ba.

- Tinubu ya fito a yau Talata yace suɓutar baki tasa ya faɗi haka amma shi 50,000 yaso ya faɗa ba 50 miliyan ba

- Wannan magana da ya yi dai a jiya wajen taron murnar cikarsa shekaru 69 a duniya ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

Jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce ba yana nufin gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja ba, 50,000 yaso faɗa bakinsa ya kuɓuce.

KARANTA ANAN: Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada

Tinubu ya gyara kalamansa ne yau Talata inda yace suɓutar baki ne yasa ya faɗi haka amma shi mutum 50,000 ya so cewa.

Andai ga Tinubu na faɗa a wani bidiyo da ya mamaye kafafen sada zumunta cewa, gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja don ta ƙarfafa yaƙin da take da ta'addanci wanda ya dabai-bayeta.

Jagoran jami'iyya mai mulki ya faɗi haka ne a wajen taron bikin cikarsa shekaru 69 a duniya ranar Litinin, 29 ga watan Maris.

"Ku ɗau matasa 50 miliyan aikin soja" Tinubu ya faɗa a wajen taron yana mai ƙarawa da cewa duk abinda zasu ci muna da su a ƙasar nan.

Kuskuren harshe ne ba haka nado faɗa ba, Tinubu ya gyara kalamansa kan ɗaukar matasa aikin soja
Kuskuren harshe ne ba haka nado faɗa ba, Tinubu ya gyara kalamansa kan ɗaukar matasa aikin soja Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada

Mai taimaka wa Tinubu ta fannin yaɗa labarai, Tunde Rahman, ya shaida cewa, yana nufin gwamnati ta ɗauki matasa 50,000 ne ba 50 miliyan ba kamar yadda ya faɗa a baya.

Sai-dai tun a jiyan da ya yi wancan magana, ta jawo hankullan mutane da yawa a kafafen sada zumunta musamman tuwita.

Ya yin da yake martani kan maganar Tinubu a jiya, tsohon sanata, Shehu Sani yace ta ya gwamnatin da ta kasa rike sojoji 150,000 zata iya ɗaukar 50 miliyan, ya kara da cewa yana mamakin yadda Tinubu ya yi wannan zancen.

A wani labarin kuma APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya

Jam’iyyar APC mai mulki ta hannun Farooq Aliyu ta yi ikirarin cewa ba ta da masaniya game da lalacewar kasar lokacin da ta karbi mulki

A cewarsa, matakin da cin hanci da rashawa ya kai abin tsoro ne, har ma ta kai abun na yakar gwamnati.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel