Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista

Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista

- Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani mai san'ar kafinta da zargin yana bata ma tsohon minista suna

- Kafintan dai yace shi ba bata masa suna yake ba yana neman a biyashi haƙƙinsa ne kawai

- Yan sandan sun ce suna gudanar da bincike akan lamarin bisa unarnin IGP na ƙasa.

Rundunar Yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani kafinta, Azubuike Osakwe, wanda ya taba aiki da tsohon ministan sufurin jirage sama Femi Fani Kayode.

An kama Osakwe ne jim kadan bayan dawowar sa daga coci ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: Bayan kwanaki 7 an sake samun gobara ta 2 da ta ci wata kasuwa a Jihar Katsina

A watan Fabrairu Osakwe ya zargi Femi Fani Kayode da kama shi lokuta daban daban a 2019 tare da hankin biyanshi kudin aikin shi

Jaridar Punch ta gano cewa yan sanda sunyi awon gaba da shi inda suka kaishi wajen binciken laifuka tare da tilasta shi yin bayani kafin su bashi beli mai tsauri.

Kafintan wanda ya ziyarci ofishin Punch tare da wasu mutane bakwai a watan da ya wuce inda suka zargi tsohon ministan da cin zarafi da kuma cin fuska.

Tsoffin maikatan gidan nasa sun kuma zargi yan sanda da tsare su lokuta daban daban bisa umurnin Femi Fani Kayode.

Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista
Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista Hoto: @PoliceNG_news
Asali: Twitter

Sun kuma yi rantsuwa tare da aje kwafi, amma duk da haka maimakon yayi bayani kan zargin da ake masa sai ya yi sauri ya shigar da tuhuma a gaban kwamishinan yan sandan Abuja, Bala Ciroma, bisa zargin bata suna.

KARANTA ANAN: 'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia

Osakwe ya fada wa Punch cewa:

"Fani Kayode ya nemi da nazo nayi masa gyara wani lokaci a 2019 a gidansa. Na kashe dubu 15 wajen gyaran injin fitar da mai, na kuma kashe dubu 42 wajen gyaran abin bandaki,

"Amma ba'a biyani kudade na ba ballantan kuma kudin aiki na."

Jami'in da ke kula da karar, CSP James Idachaba ya bayyana cewa bincike kan tsoffin ma'aikatan Femi Fani Kayode umurni ne daga kwamshinan yan sanda.

Idachaba ya bayyana cewa ma'aikatan ba'a tursasu dole su canza bayanansu ba amma dai an bincike su bisa zargin bata suna.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Juma'a, 2 ga Afrilu da Litnin 5 ga Afrilu 2021, matsayin ranar hutu don murnar bikin Ista na bana.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel