Barayi Sun Yi Wa Beyonce Satar Kayayyakin Da Kuɗinsu Ya Kai Dala Miliyan Ɗaya

Barayi Sun Yi Wa Beyonce Satar Kayayyakin Da Kuɗinsu Ya Kai Dala Miliyan Ɗaya

- Barayi sun afka wurin ajiyar kayayyaki na fitacciyar mawakiyar Amurka, Beyonce Knowles

- Rahotanni sun ce yan fashin sun sace jakunkuna da tufafi da kudinsu ya fi dalla miliyan daya

- Yan sanda sun fara bincike a kan lamarin amma kawo yanzu babu wanda aka kama

Barayi sun yi wa fitacciyar mawakiya Giselle Knowles-Carter, mai yara uku, satar kayayyaki masu daraja da kudinsu ya kai Dallar Amurka miliyan daya, The Punch ta ruwaito.

A cewar yan sandan, yan fashin sun sace jakunkuna na alfarma, da tufafi masu tsada da kudinsu ya dara dalla miliyan daya daga wurin da Beyonce ke ajiya a Los Angeles.

Barayi Sun Yi Wa Beyonce Satar Kayayakin Da Kuɗinsu Ya Kai Dala Miliyan Ɗaya
Barayi Sun Yi Wa Beyonce Satar Kayayakin Da Kuɗinsu Ya Kai Dala Miliyan Ɗaya. Photo by Chelsea Lauren/Stutterstock
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta

An kuma kai hari a wurare uku da Beyonce ke ajiya a Los Angeles a lokuta daban-daban cikin wata daya.

TMZ ta ruwaito cewa barayin sun balle wuraren ajiya guda uku a ginin, suka sace kayan wasa, hotuna, mallakar daya daga cikin mai yi wa taimakawa Beyonce wurin zaben kayan da za ta saka.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

A yayin da yan sanda ke cigaba da gudanar da bincike a kan satar, har yanzu ba a kama kowa ba.

A wani rahoton daban, kun ji cewa fusatattun yan kallo sun lakadawa alkalan wasan kwallo duka a gasar wasar Division One a wasan da aka buga a mako na 14 a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, LIB ta ruwaito.

A cewar kafafen watsa labarai na kasar Ghana, lamarin ya faru ne bayan da kungiyar Wanamafo Mighty Royals suka buga wasa da Bofoakwa Tano aka tashi wasan ba tare da an saka kwallo a ragar kowa ba.

Rahoton ya ce magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidanta sun afka cikin filin bayan an hura usur din tashi suka lakadawa jami'an wasan duka har ta kai ga rafari Niatire Suntuo Aziz ya rasa wasu daga cikin hakoransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164