Yanzu-yanzu: Abin fashewa ya kashe a kalla mutane shida a Zamfara

Yanzu-yanzu: Abin fashewa ya kashe a kalla mutane shida a Zamfara

- Wani abin fashewa ya yi sanadin halakar rayyuka shida a kauyen Magami da ke karamar hukumar Maradun

- Wasu yara da suka shiga daji nemo itace ne suka tsinci abin fashewar sannan ya fashe a lokacin da suke wasa da shi

- Guda shida cikin yaran sun mutu nan take yayin da daga bisani daya daga cikin wadanda suka yi rauni ya sake mutuwa

Ana fargabar a kalla yara shida sun rasu sakamakon fashewar wani abu a kauyen Magami da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara, The Channels ta ruwaito.

Da ya ke tabbatar da lamarin a ranar Talata, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Abubakar Dauran ya ce wadanda abin ya shafa sun shiga daji neman itace ne inda suka tsinci abin fashewar suka fara wasa da shi.

DUBA WANNAN: Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

Yanzu-yanzu: Abin fashewa ya kashe a kalla mutane shida a Zamfara
Yanzu-yanzu: Abin fashewa ya kashe a kalla mutane shida a Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Yayin da mutum shida sun mutu nan take, wasu suna nan da raunuka daban daban.

An garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibiti a Gusau babban birnin jihar nan take domin yi musu magani.

KU KARANTA: Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane

A cewar kwamishinan tsaron, daga bisani an sake sanar da shi cewa daya daga cikin wadanda ake jinyarsu a asibiti ya rasu.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakan cewa hakan ba zai sake faruwa a gaba ba.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel