Gwamnatin Nasarawa za ta yi haɗin gwiwa da mafarauta don yaƙar ƴan bindiga

Gwamnatin Nasarawa za ta yi haɗin gwiwa da mafarauta don yaƙar ƴan bindiga

- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki tare da mafarauta don yakar yan bindiga

- Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da mambobin kungiyar Mafarautar Nigeria suka ziyarce shi a gidan gwamnati

- Gwamna Sule ya shawarci kungiyoyin mafarautar su hade kansu karkashin lema guda domin a samu saukin aiki da su

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce gwamnatinsa za ta yi hadin gwiwa tare da mafarauta a jihar domin magance kalubalen rashin tsaro, News Wire ta ruwaito.

Sule ya sanar da hakan ne yayin da ya ke tarbar mambobin kungiyar mafarauta ta Nigeria a gidan gwamnati a Lafiya.

Gwamnatin Nasarawa za ta yi hadin gwiwa da mafarauta don yaƙar ƴan bindiga
Gwamnatin Nasarawa za ta yi hadin gwiwa da mafarauta don yaƙar ƴan bindiga. Hoto: @NewsWireNGR
Source: Twitter

Ya ce gwamnatisa za ta basu gudunmawa domin magance kallubalen tsaro kamar hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane.

DUBA WANNAN: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

Sule ya ce mafarauta sun dade suna aiki tare da jami'an tsaro a wasu jihohin "amma abinda ya ke fata shine ganin gwamnati ta yi aiki tare da su domin saka musu bisa sadaukar da rayyukansu wurin samar da tsaro."

Bugu da kari, ya yi kira ga kungiyar ta janyo sauran mafarautan da ba su cikinta domin a samu saukin aiki tare da su.

Sule ya kuma yi kira da sakataren kungiyar na kasa ya hada kan dukkan mafarauta a karkashin lema guda domin inganta aikinsu.

An saba samun kananan kungiyoyi daban-daban amma ina kira gare ku, ku duba yiwuwar hada kanku wuri guda domin muna girmama ku, in ji gwamnan.

KU KARANTA: Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje

Tunda farko, Joshua Shateme, Kwamandan Kungiyar Mafarauta ta Nigeria, ya ce sun kai ziyara gidan gwamnatin ne domin su gabatar da kansu ga gwamnan.

Mr Shateme ya ce mambobin kungiyar za su hada kai da gwamnan domin magance kallubalen tsaro.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Source: Legit.ng

Online view pixel