Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje

Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a iya amfani da lambar NIN don banbance makiyaya na gari da bata-gari

- Gwamnan ya ce ya zama dole a tilastawa dukkan makiyaya mallakar lambar NIN domin bayanan da ke ciki zai taimaka wurin gano masu laifi

- Gwamnan ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci a mayar da hankali wurin inganta tatttalin arzikin rayuwar makiyayan

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ce ana iya amfani da lambar shaidan dan kasa wato NIN domin gano bata gari cikin makiyaya, The Cable ta ruwaito.

Da ya ke magana yayin wata hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today a gidan talabijin na Channels, Ganduje ya ce ana iya gano muhimman bayanai daga NIN idan an yi bincike.

Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje
Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An tsige shugaban karamar hukumar PDP

Gwamnan ya ce kalilan ne cikin makiyaya suke bata gari, ya kara da cewa kallubalen shine banbancewa tsakanin bata garin da makiyaya na gari daga cikinsu.

"Idan kawai bayanai da fasaha, abin zai yi sauki (banbanci tsakanin makiyaya na gari da bata gari). Mu tabbatar an tilastawa dukkan makiyaya yin samun lambar NIN kamar yadda aka wajabtawa sauran yan kasa," in ji shi.

"Ta hanyar amfani da fasaha, za ka iya gano bata gari daga cikinsu. Da dukkan makiyaya bane bata gari, kadan ne cikinsu. Tunda dukkansu makiyaya ne, akwai wahalar banbance su.

KU KARANTA: Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fannin tsaro, in ji Gwamna Ortom

"Abinda ya fi muhimmanci shine karfafawa tattalin arzikin makiyaya Fulani. Suna bukatar tsarin kiwo na zamani, ba mu cika magana kan wannan ba. Kan tsaro kawai muke magana.

"Ba mu magana kan inganta tattalin arzikin rayuwarsu wadda hakan shima ya haifar da kallubalen tsaro."

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: