An nada Mohammed Yerima a matsayin sabon kakakin sojojin Nigeria

An nada Mohammed Yerima a matsayin sabon kakakin sojojin Nigeria

- Rundunar sojojin Nigeria ta nada sabon mai magana da yawunta, Yerima Mohammed

- Yerima Mohammed, wanda kwararre ne a fanin sadarwar zai maye gurbin Sagir Musa

- Ya rike mukamai a matsayin kakakin soji a wurare da dama ciki har da makarantar horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna

Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

An nada Mohammed Yerima a matsayin sabon kakakin sojojin Nigeria
An nada Mohammed Yerima a matsayin sabon kakakin sojojin Nigeria. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

An sa ran Yerima zai fara aiki a ranar Laraba 10 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

DUBA WANNAN: Hotunan wani da aka cafke yana fashi sanye da kayan Civil Defence

Ya shiga aikin soja ne a Oktoban 1989 sannan daga bisani ya shiga sashin hulda da jama'a na rundunar.

Yerima, wanda ke da digiri na fanin kimiyyar siyasa daga jam'iar Ahmadu Bello da ke Zaria ya yi aiki a wurare daban daban a rundunar soji.

Ya rike mukamin kakakin rundunar soji daga 1995 zuwa 1996; Kakakin makarantar horas da jami'an sojoji, NDA, daga 1996 zuwa 2000; kakakin soji a karkashin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sierra Leone daga 2000 zuwa 2002; Mataimakin shugaban sashin watsa labarai daga 2007 zuwa 2009 da kuma direktan, sashin sadarwa na tsaro daga 2009 zuwa 2013.

KU KARANTA: Buhari ya naɗa ni shugaban soji ne saboda ƙaunar da mahaifina ke masa, in ji Buratai

Yerima mamba ne na Cibiyar Kwararrun Masu Hulda da Al'umma, NIPR, Masu Hulda da Al'umma na Afirka, APRA da kuma Kungiyar West Africa Society for Administration and Communication.

Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban kwamitin sadarwa da watsa labarai na gaggawa, MICEM.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel