Hotunan wani da aka cafke yana fashi sanye da kayan Civil Defence
- Yan sanda sun yi nasarar kama wani da ake zargi da fashi da makami a jihar Ogun
- Wanda ake zargin, Adeolu Bankole, ya afka gidan dalibai ne sanya da kayan Civil Defence ya musu fashi
- Daga bisani sun kai wa yan sanda rahoto inda aka bi sahunsa aka kuma kama shi tare da kayayyakin da ya sace
Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani da ake zargi da fashi da makami, Adeolu Bankole, wanda ya yi wa wasu mutane fashi sanye da kayan aikin jami'an tsaro na Civil Defence wato NSCDC, Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi wanda ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Litinin a Abeokuta, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Juma'a 5 ga watan Fabrairu a Ayetoro da ke jihar.
A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne biyo bayan korafin da wasu daliban jami'ar OOU da ke Ayetoro suka shigar na cewa wani dan fashi ya kwace musu kayayyakinsu.
Oyeyemi ya ce wanda ake zargin ya afka gidan daliban sanye da kayan jami'an civil defence ya kwace musu wayoyin hannu da kwamfuta.
DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa
Bayan rahoton, kwamandan unguwar Ayetoro, ACP Anthony Haruna ya aike da jami'ansa su bi sahun bata garin bayan sun yi bincike sun gano inda ya buya.
"Bayan isa mabuyarsa, an gano jaka dauke da wayoyin hannu shida, kwamfuta daya, kayan civil defence da karamar bindiga pistol.
"Daga nan jami'an suka yi kwantar bauna kuma kimanin karfe 5 na yamma wanda ake zargin ya sadada ya shiga kangon da ya boye kayan ya nufi inda jakar ta ke," a cewar Oyeyemi.
Ya cigaba da cewa bayan kama wanda ake zargin da wasu kayan satar tare da shi, wadanda aka yi wa fashin sun tabbatar shine ya musu fashin.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin
Kakakin yan sandan ya ce bincike ya nuna wanda ake zargin ya sace kayan civil defence din ne daga cikin wata motar jami'in a Disambar 2020 sannan ya cinna wa motar wuta.
Kwamishinan yan sanda, Edward Ajogun ya ce a mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na CIID domin zurfafa bincike.
A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.
Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng