Buhari ya naɗa ni shugaban soji ne saboda ƙaunar da mahaifina ke masa, in ji Buratai

Buhari ya naɗa ni shugaban soji ne saboda ƙaunar da mahaifina ke masa, in ji Buratai

- Tsohon babban hafsan sojojin kasar Nigeria, Tukur Buratai, ya ce kaunar da mahaifinsa ke yi wa Buhari yasa Buhari ya nada shi mukaminsa

- Janar Tukur Buratai (mai murabus) ya yi wannan jawabin ne a wurin taron karramawa da aka shirya masa na bankwana da aiki

- Ya ce mahaifinsa wanda shima tsohon soja ne ya kasance mai kaunar Buhari don haka yana kallon nadin da aka masa a matsayin tukwici ga mahaifinsa

Tsohon babban hafsan sojojin kasar Najeriya, Lt. Janar Tukur Buratai (mai murabus) ya danganta nadinsa a matsayin shugaban sojojin saboda kaunar da mahaifinsa ke yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewarsa, nadin da aka masa a watan Yulin shekarar 2015 sakayya ne ga mahaifinsa Yusuf Buratai da Buhari ya yi masa, The Punch ta ruwaito.

An nada shi babban hafsan sojoji ne saboda kaunar da mahaifina ke yi wa Buhari, Buratai
An nada shi babban hafsan sojoji ne saboda kaunar da mahaifina ke yi wa Buhari, Buratai. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

The Punch ta ruwaito cewa mahaifin Buratai shima jami'in soja ne a rundunar Royal West African Frontier Force kuma yana daga cikin sojojin da suka yi yakin duniya na II a Burma.

DUBA WANNAN: Abin da yasa jami'an tsaro ba za su iya gano yan bindigan da Gumi ya gana da su ba, Adamu Garba

Tsohon shugaban sojojin ya mika godiya ga shugaban kasar bisa damar da ya bashi na yin aiki a matsayin shugaban sojoji, ya kara da cewa ya yi aikinsa iya kokarinsa.

Ya kuma kara da cewa duk da cewa rike mukamin shugaban sojoji abu ne mai tattare da kalubale, shugabanin sojojin sun yi nasara, ya kara da cewa, "na yi murabus amma ban gaji ba Insha Allah."

Buratai ya ce, "Mahaifina masoyin shugaban kasa ne kuma nadin da aka min matsayin shugaban sojoji, tukwici ne na kaunar da mahaifina ke yi wa shugaban kasa.

"Kamar yadda aka sha fada maka (ni da shugaban kasa) mun hadu a N'djamena kuma ya ga cewa ni ne ya dace in zama shugaban sojojin kasa a wannan lokacin mai muhimmanci da tarihi a kasar mu.

KU KARANTA: Aljamiranci ne ya samar da Dangote, Rabiu da sauransu, in ji Adamu Garba

"Kuma ina farin cikin cewa na yi iya kokari na kuma na yi aiki na bisa kwarewa da biyaya ga kasata kuma zan cigaba da yi masa da kasa na da al'umma na hidima."

Buratai ya yi wannan jawabin ne wurin taron karramawa da aka shirya masa na bankwana da aiki.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164