Shugaban majalisar dattawa ya bayyana dabi'u 4 da ya kamata shugaba ya mallaka

Shugaban majalisar dattawa ya bayyana dabi'u 4 da ya kamata shugaba ya mallaka

- Sanata Ahmad Lawan ya ce akwai wasu dabi'un da ya kamata masu rike da mukaman shugabanci a Najeriya su mallaka

- Shugaban majalisan dattawan ya bayyana wannan ra'ayin ne yayin gabatar da jawabi a kwalejin tsaron Najeriya, Abuja

- Lawan ya ce akwai bukatar hadin kai na gaske tsakanin yan Najeriya

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya lissafa abubuwa hudu da ya kamata duk wani shugaba a Najeriya ya mallaka.

Lawan, wanda dan majalisa ne daga Yobe ya bayyana wadannan dabi'u yayin gabatar da jawabi a Kwaljin tsaron tarayya dake Abuja.

Hadiminsa na sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Sadiq Usman, ya bayyana abinda maigidansa ya fada ranar 2 ga Febrairu, 2021.

A cewar shugaban majalisar dattawan, kowani shugaba na kwarai yana bukatan:

1. Ikon karfafa cigabar kasa

2. Ikon cika burukan mutane

3. Shirya sauraron mutane, da daukan mataki

4. Barin tarihi na kwarai ga yaran gobe

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa ba za'a samu cigaba a kasar nan ba sai an hada kai da juna.

DUBA NAN: Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya samu waraka daga cutar Coronavirus

Shugaban majalisar dattawa ya bayyana dabi'u 4 da ya kamata shugaban ya mallaka
Shugaban majalisar dattawa ya bayyana dabi'u 4 da ya kamata shugaban ya mallaka Credit: @NGRSenate
Source: Twitter

KU DUBA: 'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja

A bangare guda, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake ankarar da ‘yan Najeriya game da shirin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na haifar da rikicin kabilanci da addini a wasu sassan kasar.

Hukumar DSS a watan Junairu ta yi bayanin cewa wasu mutane suna aiki tare da mutanen waje don tayar da rikicin addini a fadin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel