Sabbin mutane 1,430 sun kamu da cutar Korona ranar Litinin a Najeriya

Sabbin mutane 1,430 sun kamu da cutar Korona ranar Litinin a Najeriya

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Kusan makonni uku a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, a makon da ya gabata ya bayyana cewa an yi gwajin samfuri milyan daya tun da korona ta bulla a Najeriya kuma sama da dubu dari suka kamu da cutar.

A ranar Litinin, 25 ga watan Junairu 2021, Mutane 1,430 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 122,996 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 98,359 yayinda 1,507 suka rigamu gidan gaskiya.

Sabbin mutane 1,430 sun kamu da cutar Korona ranar Litinin a Najeriya
Sabbin mutane 1,430 sun kamu da cutar Korona ranar Litinin a Najeriya Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sandan Najeriya sun fi na kowace kasa kwarewa a duniya - IGP

Ga jerin wadanda suka kamu a jihohi ranar Litinin:

Lagos-744

Plateau-100

Oyo-77

FCT-75

Nasarawa-74

Katsina-48

Edo-42

Kano-41

Enugu-37

Rivers-34

Ogun-33

Kwara-32

Niger-28

Ebonyi-27

Kaduna-26

Borno-12

Yobe-10

Ekiti-5

Gombe-1

KU KARANTA: Likitoci 3 sun mutu, 53 suna fama da Covid-19 a Kano

A bangare guda, Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa amfanin barin yara su koma makaranta ya rinjayi tsoron kamuwa da cutar Korona.

Ihekweazu ya bayyana hakan a taron kungiyar likitocin yaran Najeriya watau (PAN) ranar Juma'a a jihar Legas, The Cable ta ruwaito.

Ihekweazu ya ce lallai ya yi na'am da shawaran bude makarantu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel