Shugaba Biden ya ba jami’an Sojojin da suka canza jinsi damar aiki a Amurka

Shugaba Biden ya ba jami’an Sojojin da suka canza jinsi damar aiki a Amurka

- Jiya shugaba Joe Biden ya bude kofa ga duk masu neman shiga Soja a Amurka

- Biden ya rattaba hannu a dokar da ta ba masu canza jinsinsu damar zama Sojoji

- A lokacin da Donald Trump yake mulki ya haramta wa wadannan mutane aiki

A makon nan, shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya soke dokar Donald Trump wanda ta haramta wa mutanen da su ka sauya jinsinsu aiki a gidan soja.

Rahotanni daga BBC sun tabbatar da cewa Joe Biden ya canza wannan doka ne a ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, ya ba kowa ‘yancin yin aikin soja.

Sabon shugaban kasar ya soke wannan tsari da aka kawo a baya, ya ce: “duka ‘Yan Amurka’ da su ke da damar su shiga gidan soja, za su iya yin hakan."

Biden ya kawo wannan tsari ne a wata doka mai iko da ya rattaba wa hannu a fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Buhari ya yi waje da Ambasadan Amurka mai shekara 83, ya nada mace

“Abin da dokar ta ce shi ne jami’an da suka canza jinsinsu, ba za su cigaba da fuskantar barazanar sallama daga aiki, ko kuma a ware su, saboda jinsinsu ba.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin fadar White House ta cigaba da cewa: “Sojoji suna samun nasara ne a lokacin da aka samu mabanbantan Amurkawa da za su iya namijin aikin da aka sa.”

Gwamnatin Biden wanda ta karbi mulki kwanaki biyar da su ka wuce, ta na da ra’ayin cewa cudanya irin wannan a gidan soja, zai inganta tsaron Amurka.

Da wannan matsaya da Biden ya dauka a makon nan, an yi fatali da matakin da shugaba Trump ya dauka a 2017, na hana irin wadannan mutane aiki a gidan soja.

KU KARANTA: Biden ya sa hannu a wasu dokoki 17 bayan ya gaji Trump

Shugaba Biden ya ba jami’an Sojojin da suka canza jinsi damar aiki a Amurka
Shugaban kasar Amurka Joe Biden Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A dokar Amurka, shugaban kasa ya na da damar kawo yadda za a tafiyar da tsare-tsaren harkar tsaro.

A jiya ne ku ka ji cewa wasu manya suna kokarin sa Joe Biden ya goyi bayan Dr. Okonjo-Iweala ta hau kujerar kungiyar kasuwanci na Duniya watau WTO.

Wasu manya a Amurka sun aika takarda zuwa ga Joe Biden, su ka fada masa cewa ya kamata Ngozi Okonjo-Iweala ta zama macen farko da za ta rike WTO.

Idan za ku tuna 'Yar Najeriyar ta gamu da cikas a baya saboda rashin goyon bayan Donald Trump.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel