Joe Biden ya dakatar da aikin katangar Mexico, hana wasu kasashe shigowa Amurka, dsr

Joe Biden ya dakatar da aikin katangar Mexico, hana wasu kasashe shigowa Amurka, dsr

- Joe Biden ya sa hannu a wasu dokoki 17 bayan shiga ofishin Shugaban kasa jiya

- Biden ya maida kasar Amurka cikin WHO da yarjejeniyar 'Paris Climate Accord'

- Sabon shugaban Amurkan ya jingine maganar gina katanga saboda kasar Mexico

A ranar Laraba, shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya sa hannu a kan wasu dokoki 15 da su ke harin manufofin tsohon shugaba Donald Trump.

Jaridar New York Times ta ce wadannan dokoki da sabon shugaban kasar ya kawo sun taba sha’anin shige da fice, sauyin yanayi da kiwon lafiya.

Shugaba Joe Biden ya bayyana wannan yunkuri a matsayin tashin farko, yayin da ya shiga ofis.

Biden ya fada wa ‘yan jarida a ofishin shugaban kasa: “A halin da kasa ta ke ciki a yau, ina tunanin babu lokacin da za mu bata, a shiga aiki da gaggawa.”

KU KARANTA: Macen bakar fata ta zama Mataimakiyar Shugabar Amurka

Da wannan dokoki da shugaban ya kawo, Amurka ta koma cikin yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris Climate Accord da Donald Trump ya fitar da kasar.

Haka zalika Biden ya maida Amurka cikin tafiyar kungiyar kiwon lafiya ta Duniya watau WHO, bayan sabanin da aka samu da Trump a kan COVID-19.

A Amurka, shugaba Biden ya bada umarnin a rika rufe fuskoki tare da bada tazara a wuraren aiki.

Daga cikin sababbin dokokin da aka kawo, an dakatar da maganar gina katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico, wanda shugaba Trump ya sha alwashin yi.

KU KARANTA: Burna Boy ne kadai Mawakin Afrika da aka saurari wakarsa a bikin rantsar da Biden

Joe Biden ya dakatar da aikin katangar Mexico, hana wasu kasashe shigowa Amurka, dsr
Joe Biden Hoto: www.aa.com.tr/en/americas/biden-signs-15-orders-in-sweeping-erasure-of-trump-acts/2117501
Asali: UGC

Da wannan dokoki da aka kawo, an ajiye maganar hana wasu kasashe shigo wa cikin Amurka.

Biden ya kuma aika wa majalisa wani kudiri wanda zai bada damar yi wa bakin-hauren da su ka shigo kasar Amurka rajista a matsayin cikakkun ‘yan kasa.

A jiya ne tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fada wa jama'a cewa ‘zamu dawo’, yayin da ya bar ofis bayan wa'adinsa na shekara hudu ya cika.

Donald Trump ya yi wa jama’a jawabi kafin jirgin sama ya dauke shi zuwa mahaifarsa, Florida. Trump ya gode wa jama'a, ya kuma jero nasarorin da ya samu.

Har Trump ya yi jawabinsa ya gama, babu inda ya ambaci sunan Magajinsa, Joe Biden.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng