Mutumiyar Umuahia, Dr. Uzoma Emenike, za ta wakilci Najeriya a kasar Amurka

Mutumiyar Umuahia, Dr. Uzoma Emenike, za ta wakilci Najeriya a kasar Amurka

- Dr. Uzoma Emenike tana cikin Jakadun da aka zaba zuwa kasashen waje

- Masana sun yaba da wannan nadi da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi

- A tarihin kasar, mace ba ta taba rike kujerar Ambasada zuwa Amurka ba

A lokacin da Kamala Harris ta kafa tarihin zama macen da ta fara hawa kujerar mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Uzoma Emenike ta bar tarihi a Najeriya.

A ranar 24 ga watan Junairu, 2021, jaridar Premium Times ta rahoto cewa Uzoma Emenike ta zama macen farko da ta zama Jakadar Najeriya zuwa kasar Amurka.

Misis Emenike ta yi zarra domin babu wata mace kafinta da ta fara rike wannan babbar kujera.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi abin a yaba da ta zabi Uzoma Emenike ta zama wakiliyarta a kasar Amurka, bayan ta rike Ambasadar kasasshen Iceland da Ireland.

KU KARANTA: An yi da Buhari cewa Magajinsa zai fito daga Kudancin Najeriya

Emenike ta yi kokarin gaske a kujerar da ta rike da, wannan ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi mata sakayya da zama Ambasada zuwa kasar ta Amurka.

Misis Emenike ta fito ne daga wani gari da ake kira Umukabia-Ohuhu a yankin Umuahia, jihar Abia, ta canji tsohon Alkalin Najeriya, Sylvester Nsofor mai shekara 83.

Masana sun yaba da wannan nadin mukami da aka yi na Emenike wanda ta fara aiki da ma’aikatar harkokin kasar waje shekaru 30 da su ka wuce, har ta yi ritaya.

A 1992 ne aka nada Uzoma Emenike a matsayin Jakadar kasar Cote D’Ivoire. Bayan ta kammala wannan aiki, ta dawo gida, ta rike mukamai a ma’aikatun gwamnatin kasar.

Mutumiyar Umuahia, Dr. Uzoma Emenike, za ta wakilci Najeriya a kasar Amurka
Uzoma Emenike Hoto: www.contents101.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tinubu ya dawo Najeriya

Uzoma Emenike ta yi har Digirin PhD a jami’ar Reading ta kasar Ingila, kafin nan ta yi digiri hudu a Legas da Maiduguri a bangaren shari’a da harkokin kasashen waje.

A bara kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika jerin sunayen jakadu 42 zuwa majalisar dattawa, inda Ahmad Lawan da 'yan majalisa suka tantance su.

Daga cikin wadanda shugaban kasar ya zaba akwai Nwachukwu C. A.; A. Kefas; Y S. Suleiman; G.M. Okolo; G.E. Edopa; Muhammad A. Makarfi, da ita Uzoma Emenike.

A lokacin da aka zabi tsofaffin Jakadu, an samu rudani wajen tantance wani dattijo, Sylvester Nsofor.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel