Shugabannin Amurka sun aikawa Joe Biden takarda a game da takarar Ngozi Okonjo-Iweala

Shugabannin Amurka sun aikawa Joe Biden takarda a game da takarar Ngozi Okonjo-Iweala

- Ganin Donald Trump ya bar mulki, an dawo da maganar takarar Okonjo-Iweala

- Wasu dattawa sun roki Joe Biden ya ba Ngozi Okonjo-Iweala goyon baya a WTO

- ‘Yar Najeriyar ta gamu da cikas a baya saboda rashin goyon bayan Donald Trump

Wasu shugabanni a Amurka har da Joseph Stiglitz, sun aika wasika ga Joe Biden, suna rokon shi ya goyi bayan takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a kungiyar WTO.

A wata budaddiyar wasika da manyan suka rubuta wa sabon shugaban kasar, sun ba Jode Biden shawarar cewa za a yaba idan ya ba Ngozi Okonjo-Iweala goyon baya.

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, ana ganin cewa Duniya za ta yi wa Biden kallon ya na jawo kowa a jika idan ya goyi bayan tsohuwar Ministar Najeriyar.

Wadanda suka rubuta wannan wasika ga Joe Biden sun hada da tsofaffin jami’an gwamnatin Amurka, malaman makaranta, ‘yan kasuwa da masu zaman kansu.

KU KARANTA: Me ya yi zafi Amurka ta ke yi wa Najeriya bukulun kujerar WTO

Wadannan Bayin Allah suna so mutumiyar Najeriyar, ta zama macen farko da za ta jagoranci WTO.

Wasikar ta ce: “Muna kira domin mu karfafa maka, ka goyi bayan takarar Dr. Okonjo-Iweala, domin ta cancanci ta zama sabuwar Darekta-Janar na WTO.”

“Okonjo-Iweala gawurtacciyar mace ce, za ta jagoranci WTO wajen kawo sauyi. Ta sa kan shugabanci, ta kware a kasuwancin kasa-da-kasa, tattalin arziki, da siyasa."

Wasikar ta tike da fada wa Biden cewa: “Zaben ta a matsayin baka kuma macen farko da za ta shugabanci WTO zai aika sako ga Duniya cewa ana yi da kowa.”

KU KARANTA: Najeriya za ta tsaya wa Okonjo-Iweala a WTO - Gwamnatin Tarayya

Shugabannin Amurka sun aikawa Joe Biden takarda a game da takarar Ngozi Okonjo-Iweala
Ngozi Okonjo-Iweala Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ngozi Okonjo-Iweala wanda ta rike Ministar kudi a gida ta kai gab da zama shugabar WTO, sai aka dakatar da takarar saboda rashin goyon bayan kasar Amurka.

A baya kun ji cewa bayan ‘yan sa’o’i kadan a kan kujerar shugaban kasa ke da wuya, har an fara kawo maganar tsige Joe Biden a majalisar wakilan Amurka

Taylor Green ta gabatar da takarda, ta na neman ‘yar majalisa su tsige sabon shugaban Amurkan.

'Yar Majalisar ta jam'iyyar Republican mai hamayya tana zargin Joe Biden da aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi dafa kan kujerar shugaban kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel