'Yan bindiga sun kashe farfesa a Zaria, sun bindige dan sa

'Yan bindiga sun kashe farfesa a Zaria, sun bindige dan sa

- 'Yan bindiga a ranar Lahadi sun kutsa yankin Wusasa da ke Zaria inda suka sace Wazirin Wusasa

- Sun harbe dan sa mai suna Abdulaziz wanda ya rasu a take yayin da suka harbi wani dan sa na dangi

- A daren Litinin 'yan bindiga sun kutsa kauyen Anaba da ke Birnin Yero inda suka kashe mutum biyu

A daren Lahadi ne 'yan bindiga suka kutsa yankin Wusasa da ke karamar hukumar Zaria inda suka yi awon gaba da Wazirin Wusasa, Farfesa Aliyu Mohammed.

A take suka kashe dan farfesan mai suna Abdulaziz Aliyu yayin da suka raunata dan shi na dangi mai suna Abba Kabiru, wanda a yanzu yake asibiti, Vanguard ta wallafa.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya ce a daren Litinin ne jami'an tsaro suka kai wa gwamnatin jihar Kaduna rahoton kutsen 'yan bindiga a kauyen Anaba da ke garin Birnin Yero na karamar hukumar Igabi.

'Yan bindiga sun kashe farfesa a Zaria, sun bindige dan sa
'Yan bindiga sun kashe farfesa a Zaria, sun bindige dan sa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: UGC

KU KARANTA: 2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo wa Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a

"Wani Lawali Abdulhameed, mazaunin kauyen Anaba ya mutu bayan 'yan bindiga sun harbe shi a yayin da suka kai hari kuma yayi yunkurin tserewa.

“Hakazalika, 'yan bindiga a babura sun shiga kauyen Iyawata da ke karamar hukumar Giwa. Kungiyar 'yan sa kai sun tunkari 'yan bindigan wanda daga bisani suka tsere.

“Yan sa kan, Malam Auwalu da Alasan Shehu sun rasa rayukansu yayin wannan harin.

“Gwamna Nasir El-Rufai bayan samun rahotannin nan ya aike da gaisuwar ta'aziyya ga iyalan mamatan inda yayi musu fatan rahama. Ya yi fatan samun sauki ga wadanda suka raunta," yace.

KU KARANTA: Hotunan ministan Buhari yana yawo da sandar guragu sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, sojoji biyar da suka hada da hafsin soja daya daga bataliya ta 117, 28 Task Force Brigade ne suka rasu yayin da wasu 15 suka jigata bayan sun fadawa wani bam da mayakan Boko haram suka dasa a wani kauye da ke kudancin jihar Borno a ranar Alhamis, majiyoyi suka tabbatar.

An gano cewa lamarin ya faru wurin karfe 10:20 na safe kusa da kauyen Kwada Kwamtah Yahi da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Motar sojin Najeriyan ta bi ta kan wani gagarumin bam da mayakan ta'addancin suka dasa, ya kashe wani babban soja tare da wasu kanana hudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel