Boko Haram: Bam ya tashi da sojoji 5, wasu 15 sun jigata a Borno
- Mayakan ta'addancin Boko Haram sun dasa bam wanda ya tashi da motocin sojoji biyu a garin Chibok
- Wannan lamarin yayi ajalin sojoji biyar a take yayin da wasu 15 suka matukar jigata da miyagun raunika
- Motocin sojojin biyu kira Hilux sun je wani sintiri ne a kauyen Kwada Kwamtah Yahi da ke Chibok
Sojoji biyar da suka hada da hafsin soja daya daga bataliya ta 117, 28 Task Force Brigade ne suka rasu yayin da wasu 15 suka jigata bayan sun fadawa wani bam da mayakan Boko haram suka dasa a wani kauye da ke kudancin jihar Borno a ranar Alhamis, majiyoyi suka tabbatar.
An gano cewa lamarin ya faru wurin karfe 10:20 na safe kusa da kauyen Kwada Kwamtah Yahi da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.
Motar sojin Najeriyan ta bi ta kan wani gagarumin bam da mayakan ta'addancin suka dasa, ya kashe wani babban soja tare da wasu kanana hudu.
KU KARANTA: Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai
Wani dan sa kai, Yohanna Bitrus wanda yake daga cikin rundunar da suka tafi aikin kauyen Kwada Kwamtah Yahi, ya ce motarsu ce ta fada kan wani bam wanda ya tashi da motoci biyu kirar Hilux.
"Abun tashin hankali ne a garemu da muka je Chibok. Motar sojojin da muke tare ta fada kan wani bam kuma ta tashi gaba dayanta.
“Na ga yadda motar ta tashi sama. Amma mun yi karfin halin kwashe gawawwakin mazajen da suka mutu wanda suka hada da wani soja mai mukamin laftanal da wasu hudu.
"A kalla wasu 15 sun matukar jigata amma yanzu haka suna asibiti a Chibok inda ake duba su," yace.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust.
KU KARANTA: Shugabancin kasa: Kakakin majalisa yana nemawa Gwamna Yahaya Bello goyon baya
A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Delta Safe, a ranar 9 ga watan Janairu, sun kwace buhunhuna 1,184 na Yaraliva Nitrabor Fertilizer wuraren hanyar ruwan Effiat dake karamar hukumar Mbo dake jihar Akwa Ibom.
Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai akan sojoji, inda yace tsakanin 7 ga watan Janairun 2020 zuwa 13 ga watan Janairun lamarin ya faru, a ranar Alhamis a Abuja.
Enenche ya ce suna zargin an yi sumogal din takin ne ta wani katon jirgin ruwa na katako ta kasar Kamaru.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng