2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo wa Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a

2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo wa Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a

- Dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai ya sha caccaka tare da barazana bayan wallafa hoton mahaifinsa da na Tinubu

- Bashir ya wallafa hoton ne tare da tsokacin cewa wannan muhimmiyar hadaka ce Najeriya ke bukata, lamarin da ya janyo cece-kuce

- Wani matashi yace sai ya yi wa Bashir duka a cikin cacar bakin amma Bashir ya tabbatar da cewa harsasai 1000 za su isa garesa da tsatsonsa kafin ya kusanto shi

Bashir El-Rufai, daya daga cikin yara mazan gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya yi wallafar da ta tada kura a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Da rikicin tare da cacar bakin ta tsananta, Bashir ya ja kunnen wani matashi da yayi barzanar kai masa hari matukar sun hadu.

Lamarin ya fara ne bayan Bashir ya wallafa hoton mahaifinsa da jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu inda yace "Kudu maso yamma da arewa maso yamma. Muhimmiyar hadakar da Najeriya za ta amfana da ita."

KU KARANTA: Allah kadai zai iya tabbatar da nasarar yaki da rashin tsaro, Adesina

Kafin ka kusance ni, alburusai 1000 sun ragargaza ka da tsatsonka, Bashir El-Rufai ga wani matashi
Kafin ka kusance ni, alburusai 1000 sun ragargaza ka da tsatsonka, Bashir El-Rufai ga wani matashi. Hoto daga BashirElrufai
Source: Twitter

Wani fusataccen ma'abocin amfani da kafar Twitter mai suna @Alexjaduwa wanda ya yi tsokacin da ya harzuka Bashir, sun yi kaca-kaca.

Daga bisani, Alexjaduwa ya yi wa Bashir barazanar cewa matukar suka hadu toh babu shakka zai yi amfani da hannunsa wurin raunata masa fuska.

Bashir ya yi martanin cewa alburusai 1000 za su isa jikin Alexjaduwa tare da tsatsonsa tun kafin ya kusanto shi.

2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a
2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a. Hoto daga @Alexjaduwa
Source: Twitter

2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a
2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a. Hoto daga @Alexjaduwa
Source: Twitter

2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a
2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a. Hoto daga @Alexjaduwa
Source: Twitter

KU KARANTA: Koma: Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Najeriya

A wani labari na daban, Hadiza, matar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta bayyana alhininta akan yadda gashin dake kan mijinta ya yi furfura cikin kankanin lokaci.

Uwargidan gwamnan ta wallafa hakan ne a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu.

Hadiza ta wallafa wani hotonsu, wanda suka dauka ita da mijinta cike da shaukin soyayya. Ta alakanta furfurar mijinta da wahalhalun jihar Kaduna, bayan ta bayyana cewa shekarunsu daya, amma kuma ya fi ta tsufa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel