Hotunan ministan Buhari yana yawo da sandar guragu sun janyo cece-kuce
- Hotuna da bidiyon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yana yawo da sandar guragu sun janyo maganganu
- An ga Amaechi yana yawo da sandar guragu yayin da ya je bude wata makarantar marayu da Islamiya a Kaita ta jihar Katsina
- Makusanci Amaechi ya tabbatar da cewa gocewa ce ministan ya samu amma hakan bai sa ya hakura da ayyukan cigaban kasa ba
Ministan sufuri Rotimi Amaechi yana fama da gocewar kashi da ya samu, a cikin kwanakin karashen mako aka gano.
A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga ministan yana yawo da sandar guragu yayin bude wani gidan marayu da makarantar Islamiya a karamar hukumar Kaita ta jihar Katsina.
Duk da har yanzu ba a samu cikakken labarin abinda ya kawo gocewar kashin ba, likitoci sun gano cewa ba babban rauni bane.
KU KARANTA: Uwargidan El-Rufai ta koka da yadda wahalar mulki ta mayar da mijinta
Makusancin Amaechi kuma jigo a jam'iyyar APC, Eze Chukwuemeka Eze ya tabbatar da wannan cigaban, jaridar The Nation ta wallafa.
Eze ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan Ribas din yana samun sauki sannan yana barar addu'a daga jama'a.
Eze ya ce ganin Amaechi yana yawo da sandar guragu cike da wahala yana nuna kishin kasarsa da kuma yadda yake fatan ganin cigaban kasar.
Ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bai wa Amaechi umarnin hutawa domin samun sauki.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya
A wani labari na daban, sojoji biyar da suka hada da hafsin soja daya daga bataliya ta 117, 28 Task Force Brigade ne suka rasu yayin da wasu 15 suka jigata bayan sun fadawa wani bam da mayakan Boko haram suka dasa a wani kauye da ke kudancin jihar Borno a ranar Alhamis, majiyoyi suka tabbatar.
An gano cewa lamarin ya faru wurin karfe 10:20 na safe kusa da kauyen Kwada Kwamtah Yahi da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.
Motar sojin Najeriyan ta bi ta kan wani gagarumin bam da mayakan ta'addancin suka dasa, ya kashe wani babban soja tare da wasu kanana hudu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng