Nigeria: Abubuwa 3 da ba a taba tunanin za su afku a 2020 ba

Nigeria: Abubuwa 3 da ba a taba tunanin za su afku a 2020 ba

Shekarar 2020 ta zo ma yan Najeriya yara da manya a cikin wata siga da basu saba gani ba. Shekarar ta zo a baibai wanda ba za a taba mantawa dashi a tarihin kasar ba.

Yayinda kasar ya zo karshe, Legit.ng ta yi amfani da wannan damar wajen duba wasu abubuwan bazata da suka faru a kasar.

KU KARANTA KUMA: Manyan ayyuka 9 da ma'aikatar Pantami ta gudanar a shekarar 2020

Nigeria: Abubuwa 3 da ba a taba tunanin za su afku a 2020 ba
Nigeria: Abubuwa 3 da ba a taba tunanin za su afku a 2020 ba Hoto: Emmanuel Osodi
Source: Facebook

1. Zanga-zangar EndSARS

Ko tantama, babu wanda ya sa ran za a yi gagarumin gangamin da matasan Najeriya za su fito su koka a kan cin zarafin da yan sanda ke yi da kuma nman a rushe rundunar yan sandan da ke yaki da fashi da makami wato SARS.

Zanga zangar ya gudana a manyan birane da dama a fadin Najeriya sannan ya ja hankalin kasashen duniya.

Har ila yau, yan Najeriya a kasashen waje irinsu Amurka, Canada, Ingila, Jamus, Ireland da sauran kasashe sun shirya gangamin.

Har ya kai, maudu’in #EndSARS ya zama na daya a batutuwan da suka yi fice a soshiyal midiya.

2. Harbe-harbe da kashe-kashen masu zanga-zangar lumana a Lekki toll gate

Wannan ya kasance daya daga cikin sakamakon zanga-zangar bazatan amma babu wanda yayi tunanin afkuwar abunda aka bayyana da kisan kiyashi a wannan shekarar da wannan karni.

Amma a daren ranar 20 ga watan Oktoba, jami’an rundunar soji su bude wuta a kan masu zangar-zangar lumana a Lekki toll gate da ke jihar Lagas.

Kimanin masu zanga-zanga 12 aka rahoto cewar an kashe a yayin harbin. Rundunar sojin kasar ta musanta yin harbin.

3. Annobar Covid19

Annoba? Babu wanda ya tsammaci haka a shekarar 2020 amma sai ya afku kuma har yanzu ana cikin wannan hali.

Wannan annoba ta fara ne a 2019 a kasar China amma babu wanda yayi tsammanin cewa zai shafi fiye da mutum miliyan 78.2, lamarin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum miliyan 1.7 a duniya.

Annobar ta haddasa hargitsi a mu’amalla da tattalin arzikin duniya. Babu wanda yayi tunanin faruwar wadannan abubuwa uku a shekarar 2020.

KU KARANTA KUMA: Iyalan dan Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya sun roki FG da ta ceto shi

A wani labarin, yayinda duniya ke jiran shiga shekarar 2021 a wasu yan sa’o’i daga yanzu, tuni kasar New Zealand ta fara bikin sabuwar shekara da kayan alatu.

A wani bidiyo da shafin Bloomberg Quicktake ya wallafa a Twitter, an gano kasar ta cika da haske na alatu wanda ke nuni ga shiga sabuwar shekara yayinda mutane suka cika da farin cikin ganin sabuwar shekarar.

Sauran kasashen da suka shiga 2021 sun hada da kananan kasash irin Tonga, Samoa da Kiribati/Christmas Island.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel