Iyalan dan Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya sun roki FG da ta ceto shi

Iyalan dan Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya sun roki FG da ta ceto shi

- A lokacin da Suleiman Olufemi ya isa kasar Saudiyya, bai taba tunanin cewa zai kasance a wani lamari da zai kai shi kotu har a hana masa walwala tsawon shekaru 18

- An zargi dan Najeriyan da kasancewa cikin bata garin da suka farma wani jami’in dan sandan Saudi har suka kashe shi, inda shima aka sanya shi cikin jerin wadanda za a kashe

- Iyalansa sun roki gwamnatin Najeriya da ta kawo dauki don ceto mutumin

Iyalan Suleiman Olufemi, wani dan Najeriya da ke cikin jerin wadanda aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya tsawon shekaru 18, sun roki gwamnatin tarayya da ta kawo dauki don ceto mutumin.

Shugabar kungiyar yan Najeriya mazauna kasar waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan.

KU KARANTA KUMA: Na yanke kauna da gwamnatin Buhari, In ji kakakin kungiyar Arewa

Iyalan dan Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya sun roki FG da ta ceto shi
Iyalan dan Najeriya da aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya sun roki FG da ta ceto shi Hoto: @abikedabiri
Source: Twitter

A cewar Dabiri-Erewa, iyalan sun ziyarci NIDCOM don rokon afuwa kan Suleiman wanda aka yanke wa hukuncin kisa shekaru 18 da suka wuce.

An zargi dan Najeriyan da kasancewa cikin bata garin da suka kashe wani jami’in dan sandan Saudiyya.

Ta ce:

“Imma zai rayu ko ya mutu a yanzu ya ta’allaka ne a kan hukuncin yarinyar marigayi jami’in wacce take yar shekara biyu a waccan lokacin, amma a yanzu shekarunta 20, kuma ita ce za ta zartar da hukunci na yafe masa ko akasin haka. Minista Onyeama, hukumar Najeriya a Saudiyya da kuma wasu yan kasar a Saudiyya da @ToluSadipe na kan lamarin. An kama mutane 11, an saki dukkansu, shi kadai ne a jerin wadanda za a kashe.

KU KARANTA KUMA: Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020

“Ina ma ace ba a karfafa masa gwiwar kasancewa cikin fusatattun matasan ba. Amma za mu yi iya bakin kokarinmu, saboda albarkacin tsoffin iyayensa da iyakansa da suka zubar da hawaye ba kakkautawa a yau.”

A wani labarin, hukumar yan sandan Najeriya ta ki sakin Mulhidi, Mubarak Bala, duk da umurnin da babban kotun tarayya tayi cewa Sifeto Janar na yan sanda ya sake shi.

An kama, Bala, shugaban Humanist Association of Nigeria, a watan Afrilu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook.

A ranar 21 ga Disamba, 2020, kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala cikin gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel