Ana take mana hakin mu na sanya hijabi – Matan musulmai
- Wani kungiyar matan musulmai tayi ikirarin cewa anan take musu hakkin su
- Game da cewar kungiyar, ce musu su bayyana kunnuwa da kawuna kafin iya zama jarabawa ko rijista take hakkinsu ne na lullube jikinsu a matsayin matan musulmai
Wata kungiyar matan musulmai karkashin hakkin sanya hijabi tayi bayani a ranan Laraba,1 ga watan Febrairu, cewa ana take musu hakkinsu na sanya hijabi a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.
Kungiyar ta bayyana cewa yawancin mata masu sanya hijabi basu samun aiki da wasu dama a wannan kasa,duk da cewan sun cancanci a basu wadannan ayyuka.
Game da cewar jaridar Punch, shugabn kungiyar, Hajia Mutiat Orolu-Balogun, tace ana tilastawa matan musulmai su bayyana kunnuwansu da kawunansu kafin su zauna jarabawan JAMB ko rijistan BVN.
KU KARANTA: Soja ya hallaka wani dan achaba
Orolu-Balogun yace: “ Yi tunanin ace ka cire rigarka saboda zaka amsa lasisin tukin mota, ko ace ba zaka iya zabe ba sai kan nonuwanki ya fito a katin zabe.
“Wannan,da kuma fiye da haka ne yan matan musulmai ke fukanta idan aka ce ta cire hijabin ta kafin a bari ta zantar da hakkin dan adam din ta."
Tace sanya hijabi wajabcin addini ne ba al’adan larubawa ba da mutum zai yi lokacin da ya ga dama. Wata matar , Hajia Hafsah Badru, tayi kira ga kafofin yada labarai cewa suyi gaskiya wajen ruwaito labaan da ya shafi hijabi.
Tace: “ Gayawa ma mace ta cire hijabinta zalunci ne gareta; bai kamata a ce ana irin wannan a kasa irin Najeriya ba.”
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng